Ana yi wa muzurun da aka harba sau shida tiyata

Dante

Asalin hoton, RSPCA

Bayanan hoto,

Nan gaba za a sake yi wa Dante tiyata don cire masa harsashi uku a kusa da lakar bayansa

Ana yi wa wani muzuru tiyata bayan an harbe shi sau shida da bindiga, a bana kadai an kai masa farmaki har sau uku.

Wata cibiyar hana cin zarafin dabbobi ta RSPCA ta bayyana hare-haren da aka kai wa muzurun mai suna Dante, a kusa da gidansu da ke yankin Stoke-on-Trent cikin Ingila, a matsayin "wani aikin mamugunta".

Likitocin dabbobi sun yi kokarin ciro rabin notinan da aka yi amfani da su wajen harbin wannan mage mai shekara biyu a duniya, kuma ana sa ran zaro wasu uku da suka same shi a kusa da laka lami lafiya.

Asalin hoton, RSCPA

Bayanan hoto,

Likitoci sun ce sai an bi a hankali kafin a iya cire ragowar harsasan da aka harbi Dante da su

Mai kyanwar ya ce: "Muna ta mamaki a ce an sake kai wa Dante farmaki."

Muzurun ya koma gida ranar 5 ga watan Yuli da rauni a kwibin jikinsa.

Nan da nan, mai muzurun Zeke Ares ya garzaya da shi zuwa asibitin dabbobi, inda binciken kwakwaf na x-ray ya nuna noti shida a cikin jikinsa da aka harbe shi da su.

Mista Ares ya ce: "Wannan ne karo na uku da aka harbi Dante. Da ma an harbe shi a kafa da kuma kai.

"Muzuru ne mai shiga rai, mun kasa fahimtar abin da ya sa wani yake aikata masa haka."

Cibiyar hana cin zarafin dabbobi ta bukaci masu kyanwoyi a yankin su farga.

Wata jami'a a cibiyar Natalie Perehovsky na cewa: "Na tabbatar cewa ko ma wane ne ke yin haka da gangan yana so ne ya jikkata tare da sanya Dante cikin wahala."