An yi wa Shugaba Buhari addu'o'i a Guinea

Asalin hoton, Getty Images
A watan Maris ne shugaban ya fara jinya a Birtaniya
Al'ummar Musulmin kasar Guinea Conakry sun yi wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari addu'o'in fatan samun sauki a masallatan Juma'an kasar.
A ranar Laraba ne Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ba da umurnin gudanar da addu'o'in, a lokacin taron majalisar ministoci.
Shugaba Alpha Conde shi ne shugaban Tarayyar Afirka.
Hakazalika, kungiyar Musulmin Najeriya a Birtaniya ta gudanar da addu'o'in rokon samun lafiyar Shugaba Buhari wanda yake jinya a Landan fiye da wata biyu a ke nan.
A watan Maris da ya gabata ne aka tsara shugaba Buharin, zai kai ziyara Guinea, amma sai aka dage tafiyar tasa.
Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London