Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu kyawawan hotuna da aka zabo da sassan Afirka daban-daban da kuma wasu sassan duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata yarinya yayin da take wasa da igiyar tsallake a Cape Town da ke kasar Afirka ta Kudu inda mutane suka taru don tunawa da marigayi Nelson Mandela ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hakazalika wadannan yaran suna mika sakonsu, inda suke kira ga mutane da su bi sahun Mista Mandela wanda ya sadaukar da rayuwarsa a kan nuna adawa da wariyar launin fata da kuma jajircewa a kan hadin kai
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadannan yaran cikin shigar gargajiya a wani bikin da aka yi a filin jirgin saman Ivory Coast da ke Abidjan, bayan kasar ta mallaki sabon jirgin sama ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mawakiya Angelique Kidjo ta Jamhuriyar Benin, wacce ta lashe kyautar Grammy karo uku, wacce aka fi sani da "Africa's Premier Diva" yayin wani biki wanda ake yi shekara-shekara a Baalbeck da ke kasar Lebanon ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba'amurkiya 'yar asalin Habasha Kelela Mizanekristos, yayin da take waka a wani biki da aka yi a kasar Canada ranar Asabar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadansu mata 'yan kabilar Maasai na Kenya suke nuna alhininsu a wajen jana'izar ministan harkokin cikin gida Joseph Nkaissery ranar Asabar. An binne shi ne a kauyensu, ya rasu yana da shekara 67 sakamakon bugun zuciya.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadannan mutanen sun rufa da bargunan gargajiya ne don su ji dumi a Lesotho ranar Asabar, sun sanya kayan ne don sanyin tsaunin Semonkong, wani dan karamin gari da aka kirkira a matsayin sansanin 'yan gudun hijira, saboda kabilar Basotho da rikicin dakarun mulkin mallaka suka raba da muhallansu a shekarar 1880.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata 'yar Masar ta leko ta taga ranar Lahadi yayin da 'yarta take daukan hotunan shirye-shiryen jana'izar Syed Tafshan, wanda ya mutu bayan da aka yi hargitsi da dakarun tsaro a kan rushe gina-ginan da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadannan ne matan suka wakilci kasar Masar a wasan ninkaya a gasar wasannin ruwa ta duniya da aka yi a Budapes, babban birnin Hungary ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mata 'yan Najeriya suna girki a wata makarantar mata da ke garin Maiduguri, arewa maso gabashin kasar ranar Talata, inda mayakan Boko Haram suka tilaswa mutanen yankin da dama kauracewa muhallansu, suka koma sansanin 'yan gudun hijira.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zanen tsohon shugaban kungiyar Soviet, Josef Stalin inda aka yi ado da shi a bango wani gidan abinci mai suna, "The Dictator" a wata unguwa da ke kusa da birnin Tunis na kasar Tunisiya ranar Alhamis.
Hakkin mallakar hoto Joop Van Der Linde/Panthera
Image caption 'Yar damisa tana shan nonon zakanya a yankin wani dadadden wurin tarihi na duniya da namun daji suke a kasar Tanzaniya ranar Juma'a. Masana halayyar namun daji sun ce wanne ne karon farko da aka samu jituwa tsakanin wadannan dabbobin, domin bisa al'ada ba sa ga maciji.

Labaran BBC