Kun san 'yan wasan da kungiyoyi ke rububin dauka?

Renato Sanches

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanches ya koma Bayern Munich daga Benifa ne a shekarar 2016

Kulob din Manchester United yana zawarcin dan wasan tsakiyar Bayern Munich Renato Sanches, kamar yadda jaridar Daily Star ta ruwaito.

Da wuya kulob din RB Leipzig na Jamus ya ki sallawa Liverpool Naby Keita bisa tayin da ta yi fam miliyan 80, kamar yadda jaridar Liverpool Echo ta ruwaito.

Cinikin golan Barcelona Dutchman Jasper Cillessen da kulob din Crystal Palace yake yi ya fuskanci cikas bayan da golan ya ce yana son ci gaba da kasancewa a Barcelona, in ji Croydon Advertiser.

Arsenal za ta fafata da Tottenham wajen zawarcin dan wasan Everton Ross Barkley, kamar yadda jaridar Daily Express ta bayyana.

Ita kuma jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa Manchester City ta ce za ta kashe fam miliyan 44.5 don neman sayen Benjamin Mendy daga Monaco. Monaco tana neman fam miliyan 45.

Hakazalika, Manchester City za ta kammala sayen dan wasan bayan Real Madrid Danilo ranar Juma'a , kamar yadda Marca a Spain ta ruwaito.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Coutinho ya koma Liverpool a shekarar 2013 daga Inter Milan.

Barcelona tana zawarcin dan wasan tsakiyar Liverpool Philippe Coutinho a kan fam miliyan 72, amama na kyautata zaton cewa kulob din ba zai amince da tayin ba, kamar yadda Daily Mail ta bayyana.

Liverpool ta ce Barcelona tana bata wa kanta lokaci ne, in ji jaridar Liverpool Echo.

Arsenal tana da gwarin gwiwar cewa dan wasan tsakiyar kulob din Mesut Ozil zai sabunta yarjejeniyarsa a kulob din, in ji jaridar Sun.

Manchester United ta mayar da hankalinta a kan dan wasan Paris St-Germain Serge Aurier, da kuma Fabinho na Monaco, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Kocin Paris St-Germain ya ba da tabbacin cewa dan wasan Ivory Coast Aurier yana son barin kulob din a kakar bana, in ji jaridar Metro.

Dan wasan tsakiyar Arsenal Jack Wilshere a shirye yake ya koma West Ham - idan Arsenal ta amince da tayin da ta yi masa, in ji Daily Sun.

Tottenham ta bukaci a sanar da ita halin da ake ciki game da Riyad Mahrez na Leicester City, amma ana ganin sai an rage farashin da suka sa masa na fam miliyan 50, in ji jaridar Standard.