Duk inda Shekau yake ku kamo shi nan da kwana 40 – Buratai

Abubakar Shekau
Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya sun dade su na ikirarin sun hallaka jagoran kungiyar ta Boko Haram

Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya umarci kwamandan rundunonin da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar,, Manjo Janar Ibrahim Attahiru da ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Hafsan sojin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya aike wa manema labarai, inda ya kara da cewa an bai wa kwamandan kwanaki 40 kacal ya kawo jagoran kungiyar ta Boko Haram.

Sanarwar ta ci gaba da cewa janar Tukur Yusuf Buratai na bukatar manjo janar Attahiru ya baza sojojin da ke karkashin ikonsa lungu da sako dan zakulo Shekau a duk inda ya ke boye a Najeriya.

Haka kuma sanarwar ta bukaci 'yan kasar su sanya hannu a wannan gagarumin aiki da ake bukatar yin sa cikin wa'adin kwanaki 40 wajen bayar da duk wata shaida ko karin haske ko wani bayani da zai taimaka wa jami'an tsaro kama jagoran kungiyar.

Tayar da kayar bayan kungiyar Boko Haram dai ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya da janyo dubban 'yan kasar barin muhallansu a inda da dama suka ketara kasashen makofta domin gudun hijra.

Shekaru biyu kenan dai da hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulkin Najeriya kuma ya sha alwashin kawo karshen kungiyar Boko Haram da ta addabi kasar.

Har wa yau a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, lokacin da shugaban ya sha rantsuwar kama aiki ya mayar da rundunar Sojin kasar jihar Borno dan gudanar da ayyukansu tare da ba su wa'adin watanni bakwai su kawo karshen kungiyar Boko Haram.