Nigeria: Yajin aiki ya shafi ayyuka a CAC

Yajin aiki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aikata na da 'yancin yajin aiki a Najeriya

Al'amura sun tsaya cik a hukumar dake rijistar kamfanoni da harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commission.

Wannan ya biyo bayan yajin aikin sai-baba-ta-gani da ma'aikatan hukumar suka shiga a fadin kasar tun ranar Litinin.

Ma'aikatan na korafin shugabannin hukumar sun rage musu albashi, kuma sun danne musu wasu hakkokinsu, sannan kuma suna zargin shugabannin da almundahana.

Shugaban kungiyar kwadago reshen hukumar Ibrahim Kirfi ya yi wa BBC karin bayani kan abubuwan da suka sa su shiga wannan yajin aiki na sai abin da hali ya yi.

"Matsala ce ta taso kasancewa shugabanninmu sun rage mana albashi, amma sun kara wa kansu. Asalin abin da ya jawo matsalar kenan."

Ya kara da cewa, "Musabbabin matsalar shi ne, akwai karin albashin da tsohon shugaban kasa Goodluck yayi. Kashi 53.37 cikin dari a ka yarda za a kara ma ma'aikatu, amma mun yarda cewa a bamu karin kashi 35 cikin dari, su kuma su dauki kashi 15 domin dama kudinsu na da yawa".

Matsala ta kunno kai ne bayan shekara biyu da fara aiwatar da wannan tsarin.

Ya kara da cewa, "Sun rage mana kashi tara, sannan suka kara ma kansu kashi 11.68 a kan nasu na da. Kaga ya kara buda rata a kan albashinsu da namu."

To sai dai shugaban hukumar ta Corporate Affairs Commission, Barrister Bello Mahmud ya ce ba haka zancen yake ba.

"Albashin da suke magana wanda a ka yi kari ne tun shekarar 2010, lokacin da gwamnatin tarayya tayi karin kashi 53.5. Tun da mu ba gwamnati muke ba, sai muka tattauna da ma'aikatanmu, inda su ka yarda za su karbi karin kashi 35 bisa dari na albashinsu."

Ya kara da cewa: "Su kuma manyan ma'aikata suka ce a basu kashi 15 bisa dari kari na albashinsu."

Ya kuma ce bayan sun fara biyan karin albashin ne hukumar samar da daidaiton albashi, Salaries and Wages Commission ce ta dakatar da tsarin nasu.

"Hukumar ta dubi takardunmu, ta ce abin da muke yi kure ne, cewa bamu da ikon kara albashi ba da saninsu ba."

Ya ce daga baya hukumar ta fitar da sabon tsarin albashi, inda ta amince da, "A kara wa kowane ma'aikaci albashi kashi 26.6 cikin dari, manya da kanana."

Ya bayyana cewa wannan ne ya sa "Kananan ma'ikata su kayi asarar kashi 8 cikin dari na albashinsu", inda su kuma manyan ma'aikatan hukumar suka sami "Karin 11 cikin dari na albashinsu, dan haka su ke ganin kamar wata kulalliya aka shirya dan cutar da su, amma lamarin ba haka ya ke ba."

Ya musanta cewa ana gudanar da badakkalar kwangiloli a hukumar, "Ba mu tsoron ko yanzu a zo a duba takardunmu na kwangila, kuma duk wasu kudade da suke fadi cewa an bada kwangila ta biliyan kaza karya ce suke yi, ba su da tabbacin haka."