Kakakin fadar White House ya yi murabus

Sean Spicer
Bayanan hoto,

Sean Spicer ya yi murabus saboda an yi masa kishiya

Kakakin fadar White House, Sean Spicer ya yi murabus a wani mataki na nuna bacin ransa ga wani dan kwarya-kwaryar garanbawul da aka yi.

Kafafen watsa labaran Amurka sun ce mista Spicer ya yi murabus ne saboda rashin jin dadin yadda shugaba Donald Trump ya nada Anthony Scaramucci a matsayin sabon darektan sadarwa na fadar.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin, mista Spicer ya ce "Duk da dai mista Trump bai so na bar aikin ba amma hakan ya zama dole saboda an samu mutane da yawa a dakin girki."

A watan Agusta mai zuwa ne dai ya kamata ace mista Spicer zai bar aiki.

Ana kuma sa ran mataimakiyarsa, Sarah Huckabee Sanders za ta maye gurbinsa.

Sean Spicer dai ya fuskanci gatsali da shan suka daga Amurkawa sakamakon maganganunsa masu yawan karo da juna.

A watan Janairu ne dai mista Sean ya hau kan mukamin nasa na kakakin fadar ta White House.

Za a iya cewa wannan shi ne karo na biyu a makon nan da wani mai mukami a gwamnatin shugaba Trump ya yi murabus domin radin kansa.

Ko a ranar Alhamis ma sai da mai magana da yawun lauyoyin da ke kare shugaba Trump ya yi murabus bisa zargin ha'inci.

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a ne aka ambaci Sarah a matsayin wadda za ta gaji Mista Spicer