Man City ta sayi Benjamin Mendy na Monaco

Benjamin Mendy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mendy ya taka muhimmiyar rawa lokacin da Monaco ta lashe kofin Ligue 1 a kakar bara

Kungiyar Manchester City ta amince ta sayi dan wasan bayan kulob din Monaco Benjamin Mendy a kan fam miliyan 52.

Dan wasan tawagar Faransa wanda ya koma Monaco daga Marseille a kakar bara, ya yi wa Monaco wasa 34 kuma ya taka muhimmiyar rawa lokacin da kulob din ya lashe kofin Ligue 1 wanda ya yi shekara 17 rabonsa da dauka.

Sai dai kungiyar Manchester City ba ta tabbatar da cinikin ba tukuna.