Nigeria: Hotunan zaben kananan hukumomin Jihar Lagos

An samu karancin fitowar jama'a a jihar Legas yayin da ake gudanar da zaben kananan hukumomin jihar ranar Asabar.

Zaben Legas
Bayanan hoto,

An samu jinkiri wajen bude rumfunan zabe a wasu sassan birnin

Bayanan hoto,

Ruwan sama ya sa mutane ba su fito zaben ba sosai, kamar yadda aka saba gani a zabukan baya.

Bayanan hoto,

Akwai rahotannin da ke cewa mutane sun zauna a gida ne saboda ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wani bangare na birnin

Bayanan hoto,

Jam'iyyu 12 ne suka fafata a zaben wanda aka gudanar kananan hukumomi 20 da ke jihar

Asalin hoton, Lagos State Government

Bayanan hoto,

Masu kada kuri'a ciki har da Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode (a tsakiya) a mazabar unguwar Epe da ke birnin

Asalin hoton, Lagos State Government

Bayanan hoto,

Gwamna Ambode yayin da zai kada kuri'arsa a mazabar Epe

Bayanan hoto,

Galibin manyan titunan birnin sun kasance fayau babu zirga-zirgar ababen hawa

Bayanan hoto,

Akwai rahoton da ke cewa jami'an tsaro sun kama malaman zabe na boye biyar yayin zaben