Hari kan 'yan hijira: MSF ta yi Allah-wadai da uzurin sojin Najeriya

Boko Haram

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A watan Janairu ne jirgin sojin saman Najeriya ya yi lugudan wuta kan 'yan gudun hijira a Rann

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres, ta ce bata ji dadin sakamakon binciken da rundunar sojin Najeriya ta gudanar ba, game da lugudan wuta ta sama da aka yi akan wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane dari.

Wani kakakin ma'aikatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar John Enenche, ya ce jirgin yakin sama na sojin kasar ya kai hari kan sansanin ne, saboda ba a nuna akwai shi ba a jikin taswirar da sojojin ke amfani da ita.

Mutane 112 ne suka mutu sakamakon lugudan wuta ta sama da jirgin yakin Najeriya ya yi a sansanin 'yan gudun hijirar a watan Janairu, sannan wasu kimanin dari daya kuma suka jikkata, akasarinsu mata da yara kanana.

Tun a watan Fabrairu ne kuma aka sa ran kwamitin da rundunar sojin sama ta kasar ta kafa domin binciken lamarin zai fitar da sakamakon binciken, amma hakan bai samu ba.

Sai dai a wani takaitaccen bayani, Kakakin ma'aikatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar John Enenche, ya ce jiragen na su sun yi lugudan wuta kan sansanin ne saboda rashin babbar alama da ta nuna 'yan gudun hijira ne a wurin.

Ya ce kwamandojin sojin sun dauka cewa mutanen da suka taru a wurin, mayakan kungiyar Boko Haram ne suke shirye-shiryen kai hari.

Sai dai kungiyar Medecins Sans Frontieres, ta ce sansanin 'yan gudun hijirar, wanda yake Rann kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, sojoji sun san da zaman shi, domin su ne ke kula da shi.