Mutumin da ya yi hijira har sau biyu zuwa Turai

"Adam"

Wannan labarin wani mutum ne da ya yi nasarar boye wa 'yan sanda a kan iyakar Italiya da Faransa - har sau biyu.

Dan gudun hijiran ya sulale wa jami'an tsaro a cikin jirgin kasa zuwa birnin Paris sau biyu.

Har ila yau, ya isa matsugunin 'yan gudun hijira na Calais a Faransa - sau biyu.

Sannan ya fuskanci kalubalen rasa ransa a cikin motar da ya boye don shiga Birtaniya - shi ma sau biyu.

A halin yanzu mutumin yan tsare yana jiran hukumomin Birtaniya su yanke hukunci a kan ko yana iya zama a kasar ko kuma su sake tasa keyarsa - a karo na biyu.

Sau biyu ke nan wannan yake faruwa.

Wannan ne labarin jajircewa domin neman tsira - da dalilan da suka sa 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa nahiyar Turai.

Amma bari mu fara da labarin mutumin shi da kansa.

Bari mu kira shi Adam, saboda ba ya son na bayyana sunansa, kuma Adam domin suna ne mai farin jini a yankin Darfur na Sudan ta Kudu, yankin da ya fito.

Yana kiran kansa "dan kauye".

Amma a yau na gansa sanye da wata riga da ta sha guga, da alama Adam ya sami natsuwa a Burtaniya, duk da cewa akwai sauran rina a kaba angane da zamansa a kasar.

Bayanan hoto,

Hanyar da Adam ya bi daga Darfur a Sudan zuwa Burtaniya

Adam ya bar Darfur a shekarar 2012, inda ya fara isa Libya, kuma ya zauna na wani lokaci a can. Amma da kasar ta fara shiga rikici, sai ya yi gaba zuwa Turai.

Ya bi hanyar da dubban mutane ke bi. Daga Sicily zuwa Ventimiglia a arewacin Italiya, zuwa Paris a Faransa, daga karshe ya isa Burtaniya.

Amma kash, ba nan tafiyarsa ta kare ba.

Hukumomin Burtaniya sun tsare shi, inda suka ajiye yi har na tsawon wata hudu, kana suka sake shi.

Amma daga baya sun sake kama shi, a wannan karon sun tsare shi na wata biyu kafin daga baya suka yanke shawarar mayar da shi kasar Italiya, domin akwai shaidar cewa can ya fara sauka a nahiyar Turai.

"Sun saka mini ankwa." in ji Adam. Jami'an 'yan sanda hudu suka raka shi zuwa birnin Milan a Italiya, suka bar shi a can.

"Kwanana 10 a Milan, a titi na rinka kwana." A wannan lokacin ne ya yanke shawarar komawa Burtaniya. Ya fara komawa Ventimiglia, amma a wannan karon, lamarin yafi na farko wahala.

"Tafiyata ta fari nayi sa'a. Na shiga jirgin kasa ne kawai daga Ventimiglia zuwa Paris."

Amma a wannan karon, hukumomin Turai na sa ido sosai a kan yadda 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa nahiyar. "Sau biyu ko sau uku na gwada shiga Marseille, amma sai su hana ni shiga."

A karshe, sai ya hau kan hanyar jirgin kasa kawai, inda ya taki sayyada. "Na taka daga Ventimiglia zuwa birnin Cannes a cikin kimanin sa'a takwas." Daga nan sai ya wuce Paris, daga na kuma ya kai Calais.

A can ma wahalar ba ta kare ba. Wancan zuwan "ya fi sauki, amma a wannan karon na sha wahala saboda akwai karin 'yan gudun hijira masu yawa, kuma akwai karin 'yan sanda da suke hana su shiga."

Bayanan hoto,

Daya daga cikin hanyoyin da 'yan gudun hijira suka fi bi domin shiga Faransa

Ya gwada wucewa na kimanin "kwana 15 zuwa kwana 20", har sai da wata rana ya samu ya saka kansa a kasan wata bababr motar bas. "Sai gani a cikin Burtaniya a karo na biyu."

Adam ya koma Burtaniya bayan wata daya da kwana daya da a ka fitar da shi. Amma ba karshen labarin Adam kenan ba.

Jajircewa, kafewa, babu wata kalma da zata iya bayyana halin da 'yan gudun hijira ke ciki a hanyar da Adam ya biyo sau biyu. A ganinsa, shiga kasashen Turai ya kara zama abu mai wahala, kuma wasu ma sun yarda da Adam a kan wannan batun, kuma ga dalilin.

Kasar Italiya ce mafi yawan masu neman shiga Turai ta tekun Bahar Rum su kan nufa. Hanyar Turkiyya zuwa Girka ba ta biyuwa saboda wata yarjejeniya tsakanin tarayyar Turai da Turkiyya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bana, fiye da 'yan gudun hijira 93,000 ne suka isa Italiya.

Bayanan hoto,

Wasu 'yan ci-rani masu neman mafaka a birnin Trento dake arewacin Italiya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kasar Italiya na kokarin shiga wata yarjejeniya tsakaninta da Libya domin hana jiragen ruwa barin Libya gaba daya - amma a halin yanzu babu gwamnati a Libya, kasar da rikici ya daidaita ta.

Suna kuma neman sauran kasashen Turai dake da gaba a Bahar Rum su fara karban 'yan gudun hijiran, amma Faransa da wasu kasashen sun ki amincewa da wannan kiran.

Saboda haka ne Italiya ta raba 'yan gudun hijira zuwa sassan kasar daban-daban. Akwai matsalar da ta kunno kai a garuruwan da a ka sauke 'yan gudun hijiran sabili da yawancin su ba su iya harshen Italiyanci ba.

Wani mutum a arewacin Italiya cewa yayi, "Ba wai ba na son 'yan gudun hijira ba ne, amma ba na son yadda hukumomi ke gudanar da lamarin."

A birnin Trento kusa da iyakar Italiya da Austria, akwai wasu 'yan gudun hijira hudu daga Bangladesh, Ivory Coast, Ghana da Najeriya wadanda sun shafe kusan shekara uku suna jiran hukumomi su san yadda zasu yi da su.

"Idan da wata shida kawai nayi a nan, suka ce min zamu maida ka Ghana, da ba zan yi kuka ba", in ji Ibrahim Mohammed. Amma bayan ya shafe shekara uku fa? "Saboda me zasu ce min in koma?"

Da wuya idan za a mayar da su kasashen da suka fito, koda kuwa hukumomi sun ki amincewa da dalilansu na shiga kasar. Kadan ne a ke iya maida wa. Saura kuwa sai a bar su sun reto, babu damar yin aiki saboda basu da takardun izinin yin hakan.

Ga shi kuma kasar Italiya na fuskantar koma bayan tattalin arziki, wanda shi ne dalilin da yawancin 'yan gudun hijira ke son ficewa daga kasar zuwa wasu kasashen na Turai.

Bayanan hoto,

Nasser da dansa Aladin na neman damar zuwa wajen 'yar uwarsa dake Faransa daga Ventimiglia

Domin yawan 'yan gudun hijirar, kasashen Austria da Faransa sun baza jami'an tsaronsu domin hana su shiga kasashensu.

A cikin masu neman shiga akwai Nasser da dansa Aladin mai shekara biyu da haihuwa daga Sudan.

Aladin na fama da rashin lafiya kuma yana bukatar ganin likita.

"Sau biyu ina gwadawa a makon jiya", in ji Nasser. "'Yar uwata na Faransa, tana jiranmu. 'Yan sanda ne suka hana mu shiga."

Ita ma Faransa lamarin ya yi mata yawa, kuma suna kokarin hana wasu karin 'yan ciranin kwarara zuwa kasar.

Bayanan hoto,

Wani dan gudun hijira a Calais

Firai ministan Faransa ya sanar da wasu sabbin matakai - wadanda suka hada da saukaka tsawon lokacin da a ke dauka na tantance masu neman izinin zama a kasar.

"A cikin dubban daruruwan 'yan gudun hijira masu shiga Turai, kalilan ne ke bin hanyar da Adam ya bi zuwa Burtaniya ta Italiya da Faransa gabadayanta.

Amma bamu san ko 'yan gudun hijira nawa ne suka yi wannan tafiyar sau biyu ba.

Al'amarin Adam kuwa da sauran sarkakiya. Shekararsa guda tun bayan da ya mika takardun neman izinin zama a Burtaniya. Kuma tun daga lokacin yake gararamba, babu tabbacin ko za a bar shi ya zauna, ko kuma za a sake mayar da shi.

A halin yanzu, yana da wurin zama - wanda gwamnati ta biya masa - da kudi fam 75 a kowane mako domin biyan wasu bukatun rayuwa. Amma duk da haka yana jin kamar har yanzu tafiyarsa ba ta kare ba, kuma bai san inda rayuwa zata kai shi ba daga nan.

"Bani da aikin yi. Sai dai na ci abinci, na yi barci, shi kenan. Daga jira sai jira, babu abin da ke sauyawa. A wani lokacin sai na ji kamar ma gara na mutu kawai domin wannan ba rayuwa ce ba."