Turkiyya ta tsoma baki kan rikicin Qatar da Saudiyya

Racep Tayyip Erdogan
Bayanan hoto,

Kasashen Saudiyya, da Bahrain, da Masar da Dubai sun juyawa Qatar baya, duk da karfin tattalin da arzikin da ta ke da shi a yankin gabas ta tsakiya

Shugaban Turkiyya zai fara wata ziyarar kwana biyu a yankin Gulf, kan kokarin dinke barakar da ta sanya wasu kasashen larabawa suka juya wa kasar Qatar baya.

Racep Tayyip Erdogan zai fara isa kasar Saudiyya wadda ita ce jagaba kan zargin Qatar na taimaka wa 'yan ta'adda, kafin daga bisani kuma ya shiga kasar Kuwait wadda ta ke matsayin mai shiga tsakanin a rikicin sannan kuma ya kare ziyarar tasa a Qatar.

A watan Yuni ne kasashen Saudiyya da Hadaddiyar daular larabawa, da Bahrain da kuma Masar suka yanke duk wata alaka tsakaninsu da Qatar kan zargin taimaka wa kungiyoyin 'yan ta'adda da kyakkyawar alkakar da ke tsakaninta da Iran.

Wakiliyar BBC a birnin Santambul ta ce ya yin da shugaba Erdogan ke kokarin tsoma baki dan gyara matsalar da kokarin da ya yi na zama dan ba ruwanmu kan batun ta hanyar kin nuna goyon baya ga kowanne bangare, a bangare guda kuma ba lallai ne ya nuna goyon baya ga Saudiyya ba.

Kasashen hudu sun gindaya tsauraran sharudda 13 da suke bukatar Qatar ta yi kafin su koma mu'amala da ita, ciki har da yanke duk wata hulda da kasar Iran da rufe kafar yada labarai ta Al-jazeera.

Sai dai a na ta bangaren Qatar ta musanta dukkan zarge-zargen da a ka yi mata. Kasar dai dai ta dogara ne da kasashen waje kan abubuwan da ta ke amfani da su, da suka hada da kayan abinci.