Mahaifiyarmu mutuniyar kirki ce – Yarima William

Gimbiya Diana tare da 'ya'yan ta yarima William da Harry

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gimbiya Diana ta gamu da ajalin ta ne a wani hadarin mota shekara 20 da ta wuce

Yarima William na masarautar Birtaniya, da kaninsa Yarima Harry sun bayyana irin shakuwar da ke tsakaninsu da mahaifiyarsu marigayiya Gimbiya Diana.

Gidan talabijin din Birtaniya ya watsa wani shiri na musamman a wani bangare na bikin tunawa da mutuwar Gimbiya Diana shekara 20 da suka gabata.

Yarima William ya ce ya yi dana-sanin yadda hirar su ta karshe ta kasance da mahaifiyarsa, a lokacin da suke yankin Scotland tare da kakarsu Sarauniya Elizabeth.

Yariman ya ce sun yi magana takaitacciya cikin sauri da mahaifiyar tasa ta wayar tarho, duka 'ya'yanta sun bayyana marigayiyar a matsayi mace mai kirki da son barkwanci.

Gimbiya Diana ta gamu da ajalin ta ne a wani hadarin mota a birnin Paris a ranar 31 ga watan Agusta shekarar 1997, a lokacin Yarima William ya na da shekara 15, ya yin da kanin sa Harry ke shekara 13.

Kafin rasuwata dai sun rabu da mijinta 'ya'yanta Yarima Charles.