Nigeria: Yara uku 'yan gida daya sun mutu a mota a Kaduna

Raihan, Hamza da kuma Ikram

Asalin hoton, WHATSAPP

Bayanan hoto,

'Yan sanda suna ci gaba da bincike kan gawawwakin Raihan, Hamza da kuma Ikram

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara bincike kan mutuwar wasu yara uku 'yan gida daya wadanda aka samu gawawwakinsu a cikin wata mota a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Iyayen yaran wadanda suke zaune a unguwar Tudun Wada Kaduna sun shaida wa BBC cewa tun ranar Laraba 'ya'yansu hudu suka bace abin da ya sa "hankalinsu ya tashi."

Suleiman Hashim wanda shi ne mahaifin biyu daga cikin yaran hudu ya ce sun kwashe kimanin kwana uku suna neman Raihan, Hamza, Ikram da kuma Ilham wadanda kowannensu bai wuce shekara uku da haihuwa ba.

"A ranar Asabar ne aka same su a cikin wata mota da take gidan makwabcinmu amma dukansu babu rai idan ban ita Ilham," in ji shi.

Suleiman ya ce Ilham tana ci gaba da karbar magani a asibiti yayin da gawawwakin sauran yaran uku suna wurin 'yan sanda ana ci gaba da bincike.

Ga cikakken karin bayanin da ya yi wa BBC, sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro.

Bayanan sauti

Daya daga cikin iyayen yaran, Suleiman Hashim, yana bayanin kan yadda al'amarin ya faru.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin kuma ta ce tana ci gaba da bincike kan al'amarin.