Kun san halin da 'yan gudun hijirar Nigeria ke ciki?

Sansanin 'yan gudun hijiar Nijeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kungiyar likitoci ta MSF ta ce akwai karancin matsugunai, da wasu abin bukata kamar abinci a tsakanin 'yan gudun hijrar Nijeria da ke kasar Kamaru

Kungiyar likitocin agaji ta Medecins Sans Frontieres (MSF), ta koka kan halin da 'yan gudun Hijira daga Najeriya ke ciki bayan sun bar sansanin Minawao a jamhuriyyar Kamaru.

MSF din ta ce 'yan gudun hijiran Najeriya da suke komawa gida garuruwan Pulka da Gwoza da Banki da Bam a Najeriya bisa ga radin kansu na sake fadawa cikin halin kuncin rayuwa a kasar tasu.

Hakan ya nuna kenan zamansu a sansanin Minawao a Kamaru zai fi musu alhairi da a ce sun koma gida, saboda sabbin matsalolin da suke fuskanta.

Kana ta ce sama da 'yan gudun hijira 12,000 ne ya zuwa yanzu suka koma gida a watanni biyu da suka gabata.

Takaita zirga-zirgar jama'a da ake yi a wadannan garuruwa na dada sa wa 'yan gudun hijirar na dogaro ne kawai da taimakon da suke samu daga waje.

Kan haka ne kungiyar ta MSF ke yin kashedin cewa, ya kamata hukumomin kasar Kamaru su ja hankaln wadannan 'yan gudun hijira da ke yunkurin komawa gida cewa rayuwa a inda suke son komawa ba mai sauki ba ce saboda matsalar tsaro.

Kungiyar Boko Haram dai na ci gaba da kara kai hare-hare a irin wadannan yankuna da 'yan gudun hijirar ke ruguguwar komawa.

Shugaban 'yan gudun hijirar Nijeriyar a Kamaru Ishaq Luca, ya shaida wa BBC cewa ya zuwa yanzu hukumar lura da 'yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Kamaru da Najeriya ba su shirya mayar da su ba a hukumance.