An yi harbi kan ofishin jakadancin Israila a Jordan

Ofishin jakadancin Isra'ila a Jordan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutumin da ya mallaki ginin na daga cikin wadanda aka kashe a harin.

An kashe wasu 'yan kasar Jordan 2 aka kuma raunata wani dan kasar Isra'ila a lokacin da aka yi harbi a ofishin jakadancin Isra'ila dake Amman, babban birnin kasar Jordan.

'Yansanda sun ce mamatan 2 suna aiki ne a wata masana'antar yin kujeru kuma sun shiga ofishin ne kafin yin harbin.

Babu dai wani karin bayani game da abin ya ja aka yi harbin, amma jami'an tsaro sun toshe hanyoyin zuwa ofishin kuma Isra'ila ta kwashe ma'aikatanta.

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce wani dan kasar Jordan ne ya kai wa wani mai gadin ofishin hari da wata kusa a ginin da ofishin jakadancin ke amfani da shi.