Harin sansanin 'yan gudun hijira na Dalori ya hallaka mutane

'Yan gudun hijira na yawan kokawa kan rayuwar kunci da suke yi a sansanoni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijira na yawan kokawa kan rayuwar kunci da suke yi a sansanoni

Hukumomi a Najeriya sun ce wasu 'yan kunar-bakin-wake sun kai hari a wasu sansanonin 'yan gudun-hijira guda biyu da ke kusa da garin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gaabashin kasar.

Maharan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla hudu tare da jikkata wasu kusan 20.

An kai hare-haren ne ranar Lahadi da daddare da kuma safiyar Litinin din nan a sansanin da ke Dalori 1 da Dalori 2.

Rahotanni sun ce ana ganin a kalla daya daga cikin maharan mace ce.

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake gargadin cewa matsalar karancin abincin da yankin na arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta ka iya kara kazancewa daga yanzu zuwa watan Agusta.

Dubun-dubatar jama'a ne wadanda hare-haren kungiyar 'yan Boko Haram, masu ikirarin jihadi, suka tilasta wa barin gidajensu, ke zaune a sansanonin gudun hijira.