Cutar AIDS: Wani yaro ya warke a Afirka ta Kudu

HIV virus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaron ya kamu da cutar ne a daga mahaifiyarsa a lokacin da aka haife shi

Likitoci a Afirka ta Kudu sun ce wani yaro dan shekara tara da haihuwa, wanda ya kamu da kwayoyin cutar HIV, mai karya garkuwar jiki, a lokacin haihuwa, a yanzu ba a ganin alamun cutar a jikinsa.

An dai ba wa yaron, wanda ba a bayyana ko wane ne ba, kwayoyin rage kaifin cutar, tsawon wasu 'yan watannin farkon haihuwarsa, domin gwaji, amma tun bayan wannan ba a yi masa wani magani ba na cutar.

A yanzu haka yaron ya shafe shekara takwas da rabi ba tare da alamun kwayoyin cutar HIV ba.

Rahotanni sun ce iyayen yaron sun yi matukar farin ciki game da lamarin.

Yawancin mutane na bukatar magani kullum domin hana kwayar cutar HIV karya garkuwan jikinsu, lamarin da ke jawo AIDS

Gane yadda yaron ya samu kariya ka iya taimakawa wajen samun magunguna ko kuma riga kafin da zai dakile HIV.

Yaron ya kamu da cutar ne daga mahaifiyarsa a lokacin da aka haife shi a shekarar 2007. Yana da kwaoyin cutar HIV din da yawa a jikinsa a lokacin.

A lokacin da yaron ya kamu da cutar ba ya cikin ka'ida byar da maganin da ke dakile girman HIV a farkon rayuwa, amman an bai wa yaron maganin a lokacin da yake da makon tara da haihuwa a matsayin wani mataki na gwajin magani.

Sai aka gane cewar matakin kwayoyin cutar HIV ya yi kasa a jikinsa sosai ta yadda ba za a iya gane su ba.

Sannan aka daina masa maganin bayan mako 40. Kuma ba kamar sauran wadanda aka yi wa irin wannan maganin, cutar ba ta dawo masa ba.

Sau biyu ana samun irin maganin da ake amfani da shi a farko-farkon kamuwa da cutar yana da illa ga yara.

An fara yi wa wata 'yar jihar Mississipi ta Amurka sa'o'i 30 bayan haihuwa kuma ta shafe wata 27 ba tare da magani ba kafin cutar ta sake kunno kai.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An kuma samu wani lamari a Faransa inda kawo yanzu wani majinyaci ya shafe shekara 11 ba tare da magani ba.

Dr Avy Violari, shugabar sashen bincike kan lafiyar yara a cibiyar Perinal ta bincike kan cutar HIV da ke birnin Johannesburg, ta ce: "Ba mu yi imanin cewar maganin hana girman kwayoyin cutar HIV kawai zai iya rage cutar ba.

"Bamu san dallilin da ya sa wannan yaron ya samu saukin nan ba- mun yi imanin cewar lamarin na da alaka da kwayoyin halittarsa da garkuwar jikinsa."

'Tamkar warkewa'

Wasu sun fi wasu iya jure wa kwayar cutar HIV. Amman abun da yaron yake da shi ya sha bamban daga abin da aka taba gani.

Sabunta abin da yaron yake da shi a matsayin wani magani ko kuma riga kafi zai iya samun damar taimakawa wa sauran majinyata.

Duk da cewar babu wata kwayar cutar HIV mai aiki a jikin yaron, an samu kwayoyin halittar garkuwan jikinsa.

HIV ka iya buya a cikinsu - abun da ake ce wa HIV mara aiki - na tsawon lokaci, saboda haka akwai fargabar cewar yaron zai iya bukatar magani nan gaba.

Ma'aikatan da suka yi aikin a birnin Johannesburg sun yi aikin ne tare da bangaren gwajin magani na cibiyar binciken magani ta Birtaniya.