Shugaba Buhari zai koma Nigeria nan da mako biyu — Rochas

Bayanan sauti

Ku latsa nan domin sauraren hirar da BBC ta yi da Gwamna Rochas

Gwamnan jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, Rochas Okorocha, ya ce nan da mako biyu Shugaban kasar Muhammadu Buhari zai koma gida daga jinyar da yake yi a Landan.

Mista Okorocha, wanda na daga cikin gwamnoni hudu da suka ziyarci shugaban, ya shaida wa BBC cewa "muna ganin daga nan zuwa sati biyu insha Allah zai koma gida ya ci gaba da aikinsa".

Gwamnan ya kara da cewa shugaban yana cikin koshin lafiya "kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin halin ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau."

"Na yi mamakin yadda na gan shi. Yana da koshin lafiya. Abubuwan da ake cewa game da rashin lafiyarsa ba haka muka gani ba," in ji gwamnan na jihar Imo.

Tawagar da ta ziyarci shugaban ta hada da gwamna Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa, da Nasir Elrufai na jihar Kaduna da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi. Sai kuma Shugaban Jam'iyyar na kasa Cif John Oyegun da Ministan Sufuri Rotimi Ameachi.

A cewar Mista Okorocha sun dauki kimanin sa'a guda suna cin liyafa tare da shugaban kasar a bayyanarsa ta farko a bainar jama'a tun bayan da ya tafi jinya a birnin London kwanaki 78 da suka gabata.

Ya kara da cewa "Shugaba Buhari ya gaya mana cewa da zarar likita ya sallame shi zai komo gida. Kuma da ni ne likitan zan sallame shi ganin yadda jikinsa ya yi kwari".

Bayanan bidiyo,

Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da wannan ganawar, mai ba shugaban shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya ambato Gwamna Rochas Okorocha na cewa shugaban na cike da annashuwa kuma har yanzu yana nan da halayyarsa ta yin raha da mutane.

Gwamnan ya ce tawagar tasu ta dauki kimanin sa'a daya tana liyafa tare da shugaban kasar, kuma inji shi daga tattaunawar da suka yi ga dukkan alamu yana sane da dukkan abubuwan da ke faruwa a gida Nigeria.

Mista Okorocha ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa da ziyarar tasu kuma ya tambayi ko wnane daga cikin gwamnonin abin da ke faruwa a jiharsa.

Sanarwar ta ce da suka nemi jin abin da zai ce game da suka da miyagun kalaman da wasu 'yan kasar ke furtawa game da halin da yake cikin, sai ya yi dariya kawai tare da bayyana abubuwan da ake fadan a zaman karairayi, ya kara da cewa abin da shugaban ke jira kawai shi ne likitocinsa su bashi dama ya dawo gida.

Hoton da fadar shugaban ta saka a shafinta na Twitter dai ya nuna shi sanye da jamfa da wando bakake, da shudiyar hula, da kuma farin tabarau; yana murmushi a gaban wani teburi da aka jera wa abubuwan sha da kuma ayaba.

Ziyarar gwamnonin dai na zuwa ne kwana 12 bayan da mataimakinsa - wanda ya bar wa rikon kasar - ya kai masa wata gajeruwar ziyarar kuma ya shaida wa al'ummar kasar cewa mai gidan nasa na samun sauki cikin sauri kuma zai dawo kasar ba da jimawa ba.

Bayanan hoto,

A farkon shekarar nan ma Shugaba Buhari ya yi jinyar mako bakwai a London

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

  • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
  • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
  • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
  • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
  • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
  • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
  • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
  • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
  • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
  • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London