Isra'ila za ta cire shigen tsaro a masallacin Bait Al Mukaddas

Jerusalem

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan matakin ya fuskanci da turjiya daga Falasdiwa, abin da har ya kai ga mutuwar Falasdinawan 3 .

Jami'an tsaron Isra'ila sun yanke shawarar cire na'urorin binciken kwakwaf da suka saka a masallacin Kudus, matakin da ya kawo karuwar zaman tankiya tsakanin Falasdinawa da Yahudawa.

Wannan ya biyo bayan da Majalisar Ministocin Isra'ila ta amince da hakan amma tare da fito da wasu matakan tsaro da za su maye gurbinsu.

An dai saka na'urorin binciken ne a kofar shiga haramin na Baitul Mukaddis mai tsarki ga duka musulmai da yahudawa da nasara ne, bayan wani dan bindiga ya harbe wasu 'yan sandan Isra'ila biyu da ke tsaron wajen a farkon watan nan.

Mahukuntan Isra'ila dai sun dauki matakin ne domin hana 'yan bindiga shiga da makamansu cikin masallacin.

Sai dai matakin ya janyo jerin zanga-zanga da arangama da jami'an tsaro musamman ranar Jumu'ar da ta gabata.

Dama dai manzon Majalisar Dinkin Duniya zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, Nikolay Mladenov, ya yi gargadin cewa dole ne a warware wannan takaddama kafin wata Jumu'ar in ba haka ba lamarin zai kara muni.

''Abu ne mai matukar muhimmanci a samo bakin zaren warware wannan takaddamar kafin ranar Jumu'a ta wannan makon, domin ina ganin rikicin da ke kwance a kasa zai iya tashi idan muka yi wata Jumu'a ba tare da warware rikicin ba.''

Mr. Mladenov ya ce idan ba a yi wa tufkar hanci ba cikin sauri, to tashin hankalin zai iya bazuwa zuwa sassa daban-daban na duniyar musulmi, yana mai kara cewa:

''Ba wanda zai musun cewa lamarin hatsaniya ce irin ta unguwa amma kuma tana tasiri ga miliyoyi ko biliyoyin mutane a sassa daban-daban na duniya.''