Me ya sa ake rikici kan masallacin Kudus?

Church of the Holy Sepulchre Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Majami'u daban-daban na kiristoci ne ke ibada a cocin

Ana ci gaba da tayar da jijiyar wuya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa game da makomar masallacin Kudus, daya daga cikin wuraren da suka fi ko wanne jawo ce-ce-ku-ce a gabas ta tsakiya.

Birnin Kudus na da muhimmanci ga addinin Yahudawa da na Kiristoci da kuma na Musulmi, addinai ukun da ke da nasaba da Annabi Ibrahim (AS).

Kudus- Suna ne da yake da jan hankalin Musulmi da Kiritoci da Yahudawa a daruruwan shekarun da suka shafe suna zama tare da kuma ce-ce-ku-ce kan birnin.

A harshen Yahudanci ana ce wa birnin Yerushalayim kuma a Larabci ana ce masa al-Quds, yana daga cikin biranen da suka fi dadewa a tarihi.

Sau da yawa an ci birnin da yaki tare da lalata shi.

Kazalika an sake gina shi sau da yawa. Ko wanne mataki na kasan birnin na dauke da wani bangare na tarihin birnin Kudus.

Image caption Manyan wuraren ibada a tsohon birnin Kudus

Duk da cewar duk birnin ne silar daya daga cikin abubuwan da suke jawo ta da jijiyar wuya tsakanin mabiya addinan uku, dukkansu sun yi tarayya kan girmama wannan wuri mai tsarki.

Tsohon birnin Kudus yana tsakiyar birnin ne a yanzu inda kwaroro-kwaroro masu yawa da kuma tsarin gine-gine na tarihi sun bambance bangarorin Kiristoci da na Musulmai da na Yahudawa da kuma na Aarmeniyawa.

Tsohon birnin yana kewaye ne da wata ganuwa mai kama ta dutse kuma tana dauke da wasu wurare mafiya tsarki ga al'ummun duniya.

Ko wacce unguwa na wakiltar al'ummarta ne. Kiristoci na da unguwanni biyu saboda Armeniyawa ma Kiristoci ne kuma unguwarsu - wacce ta fi kankanta cikin hudun - daya ce daga cikin tsoffin cibiyoyin Armeniyawa a duniya.

Wani abu ne na daban saboda al'ummar Armeniyawa sun adana al'adarsu cikin Majami'ay St James wadda ta kunshi da yawa daga cikin unguwarsu.

Majami'ar

A cikin unguwar Kiristoci akwai Majami'ar da ake ce wa Church of the Holy Sepulchre a turance, wadda take da muhimmanci ga Kiristoci a fadin duniya. Majami'ar na wani wuri da aka yi imanin cewar yana da alaka da labarin Annabi Isa (AS).

Da yawan Kiristoci sun yi imanin cewar an gicciye Annabi Isa ne a wurin nan tsaunin Golgotha, ko kuma tsaunin Calvary, inda suka yi imanin cewar inda aka binne shi yana wajen da ake ce wa sepulchre din, kuma ta nan ne suka yi imanin cewar ya tashi.

Wakilai daga majami'u daban-daban, ciki har da Cocin Girka da ta darikar Katolika da ta Armeniyawa da ta Kibdawa ne suke gudanar da lamuran cocin.

Majami'ar daya ce daga cikin wuraren ibada ga miliyoyin Kiristoci da ke zuwa bauta inda suka yi imanin cewar an bunne Annabi Isa (AS) domin neman kwanciyar hankali da kuma tabarruki ta addu'a a wurin.

Masallacin

Unguwar Musulmai ita ce unguwa mafi girma daga cikin unguwanni hudu kuma a cikinta akwai Qubbat al-Sakhrah da massalacin Al-aqsa da ke kan wani tudu wanda Musulmi suka fi sani da Haram al-Sharif, ko kuma wuri mai tsarki.

Masallacin shi ne masallaci na uku a tsarki cikin addinin Musulunci kuma yana karkashin gudanarwar wani kwamitin amintattu da ake kira Waqf.

Musulmi sun yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya taho nan daga Makka a daren Isra'i da Mi'iraj kuma ya ja dukkannin Annabawa sallah.

Wasu 'yan taku kadan daga wannan wuri a Qubbat al-Sakhrah akwai wani dutsen da Musulmi suka yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya tashi zuwa sama bayan sallar.

Musulmai su kan ziyarci wannan wuri mai tsarki a ko wane lokaci cikin shekara, amma ko wacce ranar Juma'a a cikin watan Ramadan dubun-dubatar musulmi na zuwa domin su yi sallah a masallacin.

Bangon

A cikin unguwar Yahudawa akwai wata katanga ta yammaci da ake ce wa Kotel, ko kuma katangar yammaci, sauran katangar hana zaizayar tudun da ada wurin ibadan Yahudawa ke zaune.

A cikin wurin ibadar akwai inda ake ce wa Holy of Holies a turance, wato wuri mafi tsarki a addinin Yahudanci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yahudawa suna fuskantar bangon yamma ne domin gabatar da addu'o'insu

Yahudawa sun yi imanin cewar nan ne tushen inda aka halicci duniya, kuma inda annabi Ibrahim (AS) ya nemi ya yi hadya da dansa annabi Is'hak (AS). Wasu da dama kuma sun yi imanin cewar inda Qubbat al-Sakhrah yake a yanzu nan ne wuri mafi tsarki a addininsu wanda ake ce wa Holy of Holies.

A yau katangar yammaci ita ce wuri mafi kusa da Yahudawa za su iya ibada ga wuri mafi tsarki a gunsu da ake kira Holy of Holies.

Limamin Yahudawa na katangar yammaci shi yake lura da lamura a wannan wuri, kuma a ko wacce shekara miliyoyin baki na zuwa wurin katangar. Yauhudawa daga fadin duniya sukan ziyarci wannan wuri a lokacin hutun Yahudawa da ake ce wa High Holidays a turance domin yin addu'a da kuma tunawa da tarihinsu.

Rikicin baya-bayan nan

Ranar 14 ga watan Yulin nan ne wasu Larabawa 'yan Isara'ila suka kashe 'yan sandan Isra'ila biyu ta hanyar bude musu wuta a cikin harabar masallacin.

Saboda haka sai Isra'ila ta tsaurara matakan tsaro a hanyar shiga masallacin. Matakan sun hada da kafa na'urar gano karfe.

Amman wannan matakin bai yi wa Falasdinawa dadi ba domin sun fito suna zanga-zangar kin wannan mataki da suke gani a matsayin wani yunkuri na Isra'ila na neman iko da masallacin.

Kuma an samu arangama tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila kan wannan matakin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun daga ranar da hukumomin Isra'ila suka gindaya sabbin matakan tsaro a hanyar masallacin ne aka fara sallar juma'a a wajen masallacin kudus

A dai-dai lokacin da ake zaman dar-dar kan lamarin sai Isra'ila ta kafa na'urar nada bidiyo (CCTV) a masallacin.

Wannan ya sa kwamitin amintattun da ke lura da masallacin ya ce Musulmai su kaurace wa sallah cikin Masallacin har sai Isra'ila ta janye matakan tsaron da ta gindaya.

Matakan da Isra'ila ta dauka sun sha suka daga Musulmai a sassan duniya.

A ranar Litinin kuma, Majalisar ministocin Firai ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu, ta amince da a janye na'urar gane karfen da aka saka a hanyar shiga masallacin, amman za ta ci gaba da sa ido daga nesa.

Amman kwamitin amintattun da ke lura da masallacin ya ce Musulmai za su ci gaba da kaurace wa masallacin domin Isra'ila ba ta cire na'urar nadar bidiyo (CCTV) ba.

Isra'ila ta mamaye wurin da ke gabashin birnin Kudus ne tun yakin Gabas Ta Tsakiya na shekarar 1967.

Labarai masu alaka