Hotunan zanga-zangar neman bai wa matasa damar shugabanci
Daruruwan matasan Najeriya sun bazu kan titunan kasar domin gabatar da gangamin kin amincewa da watsi da kudurin da zai bai wa matasa damar takarar mukaman siyasa a kasar.

Daruruwan 'yan Najeriya sun yi ganagami a kan titunan babban birnin kasar Abuja, kan watsi da kudurin da ya bai wa matasa damar takarar mukaman siyasa.
Matasan suna neman a ceci kudurin da zai ba su damar tsayawa takarar mukaman siyasa ba sai sun kai wasu shekaru na manyanta ba.
Masu gangamin sun fara tattakinsu ne daga dandalin Unity Fountain inda suka nufi majalisar dokokin kasar.
A gangamin har da masu nakasa ma ba a bar su a baya ba.
Matasan sun wuce ta gefen babbar sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja suna dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce.
Masu zanga-zangar sun ce in har dan shekara 18 zai iya ka da kuria, to ya kamata a ba shi damar da zai iya tsayawa takara.
Matasan suna zanga-zangar ne gabanin fara kada kuri'ar da 'yan majalisa za su yi a ranar Talata na sauya wasu ayoyin doka na kundin tsarin mulki.
Ruwan da aka yi da safiyar Talata bai hana masu zanga-zangar fita maci ba suna tafe suna wake-wake da raye-raye.
Masu zanga-zangar sun zo ne daga kungiyoyin matasa daban-daban daga sassan kasar na Arewaci da Kudanci.
Ga alama wannan zanga-zanga na nuna cewa matasa sun yunkuro don ganin an dama da su a al'amuran siyasa da gwamnati.