''Yan Nigeria ne fiye da rabin yaran duniya da ba sa makaranta'

Yara 'yan gudun hijira na karbar abinci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu na daga cikin kananan yara miliyan 10 da rabi da ba sa zuwa makarantar boko a kasar

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan alkaluman da ke cewa fiye da rabin kananan yaran da ba sa zuwa makarantar boko a fadin duniya, sun fito ne daga kasar.

Yayin gabatar da jawabi a taron majalisar kasar kan sha'anin ilmi karo na 62 a Najeriya, Babban Sakataren ma'aikatar ilmi, Adamu Hussaini ya ce a cikin kananan yara kimanin miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a duniya, kaso mafi yawa na miliyan 10.5 suna Najeriya.

Ya ce: "Duk da gagarumar gudunmawa daga hukumomin ba da agaji da kuma kokarin da gwamnati ke yi don shawo kan matsalar, amma har yanzu yara kalilan ne ke zuwa makarantar Boko.

Baya ga karancin samun shiga da na kammala makarantun a tsakanin rukunin al'ummomin da aka mayar da su gefe da kuma wadanda ke da bukatar agaji.

A cewarsa, gwamnatin Najeriya ta yi imani cewa babu kasar da za ta samu budin arziki, ba tare da wani ingantaccen tsarin ilmi mai tasiri da ke ba kowa dama don a tafi da shi ba.

Hakan kuwa ba za ta samu ba, sai da tabbataccen tsaro da kwanciyar hankali a kasa.''

Adamu Hussaini ya ce kananan yaran da wannan matsala ta fi shafa sun hadar da: 'ya'ya mata da almajirai da 'ya'yan Fulani makiyaya da 'ya'yan masunta da manoman da ke kaura da kuma yaran da ke gararamba a kan tituna da sauransu.

Sauran su ne 'ya'yan nakasassu da kuma a baya-bayan nan, yaran da rikicin ta-da-kayar-baya ya raba da gidajensu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yarinyar da ke fafutuka don ganin yara mata sun sami ilimi Malala Yousafzai ta ziyarci Najeriya a makon da ya gabata

A cewar babban sakataren batun samar da kudi na da matukar muhimmanci ga bunkasar ilmi a Najeriya.

"Gwamnatin Najeriya a karkashin dokar ilmin bai-daya ta 2004, na ba da kashi 2% daga dunkulallen asusun tara kudaden shigarta don aiwatar da shirin ilmin bai-daya," in ji Adamu Hussaini.

Don haka ya bukaci taron ya bullo da hanyoyin magance matsalolin da suka shafi halin ko-in-kula da bahagon tunanin da ake yi wa yara masu bukata ta musammam.