Ana iya rayuwa da cin naman daji da 'ya'yan itace kawai?

Hadza man carrying meat on a stick

GARGADI: Sai a yi hattara da hotunan dabbobin da aka kashe.

Al'ummar Hadza na daya daga cikin kabilun da suka dogara da farauta wajen rayuwa a duniya. Ana jin suna rayuwa ne a yankin guda a arewacin Tanzania ta hanyar cin 'ya'yan itatuwa dangin magarya da kanya da rogon daji da kuma farautar dabbobi irin daban-daban tsawon shekara 40,000. Wakilin BBC Dan Saladino ya fita don ganin yadda suke farauta da fafutukar neman abinci, tare da tambayar ko nau'in abincin da suke ci ka iya zame wa kowa darussa.

Dan Saladino ya ce yayin da na kwanta rub da ciki, na sanya kaina ina kallon cikin wani rami mai duhu tare da shinshina kasar ciki.

Naman daji...

Sai dai na kasa yarda cewa mutum zai tura kansa ciki don ciro naman dajin da ke ciki. Mutumin dai shi ne Zigwadzee. Naman dajin kuma? Bushiya ce.

Bayan ya ba da ajiyar kwari da bakarsa da kuma gatarinsa na shan zuma ga wani abokin farautarsa, Zigwadzee ya tube riga, inda ya dauki wata gajerar sanda da aka fike ya shige cikin ramin.

A tunanina, an tura Zigwadzee ne saboda shi ne mafi kankanta, amma kuma na fahimci cewa an tura shi ne saboda bajintarsa, don kuwa akwai yiwuwar samun macizai ko ma ita bushiyar ta harbo kaya.

Har a wannan lokaci, ganye ne cimar kabilar Hadza, kuma sukan tsinki 'ya'yan itatuwa, lokacin da suke tafiya cikin Kungurmin dajin savannah, wanda ke cike da kaya da busassun ciyayi.

Bayanan hoto,

Matan kabilar Hadza kan tattaro 'ya'yan itace da dangin doya, a matsayinsu na abincin yau da kullum

Muna hako doya mai taushi, mu gasa a wuta domin ci, mun kuma samu bishiyar kuka, inda muka yi ta shan 'ya'yanta, wasu farare da ke dauke da dumbin sindaran Bitamin C.

Bayanan hoto,

'Ya'yan bishiyar kuka na da dimbun sinadarin Bitamin C

Masana ilimin tarihi sun gano cewa mutanen Hadza sun yi shekaru aru-aru suna neman abin kai wa baki, amma ba su taba fama da matsalar yunwa ba, saboda yanayin cin abincinsu ya samu kwarin gwiwa da yalwar ire-iren abincin da suke da su a yankin, ga su kuma gwanayen farauta.

Ga cima a wadace sai dai ni ba ma na iya gane wanne ne abin ci, amma sai ka ga yaran kabilar Hadza, wadanda wasunsu ba su wuce shekara hudu ba, sun je sun samo.

Daga can nesa sai na fara jiyo muryar Zigwadzee, inda ya kutsa cikin ramin da ya yi nisan mita biyu karkashin kasa, ga kuma wasu hanyoyi iri-iri, da bushiyar takan buya.

Bayan ya gane inda dabbar take ta hanyar bin sawunta a ramin, sai ya bayar da umurni ga wadanda ke waje su toshe sauran ramukan, don kada ta tsere.

Can bayan minti 40 sai ya fito daga ramin, budu-budu da kura da kudaje sun baibaye shi, yana kuma shirin sake kutsawa inda bushiyar ta makale a ciki.

Bayanan hoto,

Ana dasa sanduna jikin bishiyar Kuka, domin saukin hawa a debo zuma a cikin amiya.

Duk da yake, kabilar Hadza sun kai yawan mutum dubu daya mata da maza da yara, cikinsu akwai mafarauta 200 zuwa 300 wadanda ba sa noma kwata-kwata, ko kuma wani abu mai alaka da noma.

Wadannan mafarautan suna mamakin manoma kwarai da gaske, inda wani cikinsu yake tambaya ta:

"Wai ta yaya mutum zai tsaya a gona cikin rana kwana da kwanaki yana jiran abinci ya tsiro? bayan ga 'ya'yan itatuwa nan birjik a daji, ga zuma nan da yawa da za ka iya sha, ko kuma ka shiga rami cikin sa'a daya, ka kama bushiyar da za ta ciyar da rukunin jama'a guda?"

Hakan shi ne yadda iyayenmu ke neman abincin su a da. Nau'in abincin da Zigwadzee da 'yan'uwansa na kabilar Hadza ke ci, shi ne abin da ya rage na alakar abincinmu na yanzu da na mutanen da ke ci, wanda a cewar masanan kimiyya, ya nuna yadda tsarin taswirar cikin mutum ya sauya a yanzu, ciki har da nau'o'in bakteriyar da ke cikin dan'adam.

Haka kuma kabilar Hadza na da mafi yawan bakteriyar ciki a tsakanin dan'adam, saboda irin nau'in abincin da suke ci.

Bayanan hoto,

Sai an yi amfani da baka mai dafi wajen harbin dabbobi da suka kai girman alfadari

Bayanan hoto,

Jakin dawa ya fi saukin farauta lokacin rani, saboda babu wuraren shan ruwa sosai...

Bayanan hoto,

... amma kuma sun soma bacewa, saboda yadda manoma ke tsorata su

Cikin abokan tafiyar tawa har da Tim Spector, Farfesa a fannin kwayoyin halitta na jami'ar Kings College da ke London, wanda ke ta kwakwar sanin ko idan ya koma cikin nau'in abincin kabilar Hadza, cikinsa ka iya zama irin nasu.

Don haka ne ya debi samfurin kashinsa don yin gwaji, bayan ya kwana uku yana cin irin abincinsu, da nufin duba ko nau'in bakteriyan da ke jikinsa ya sauya.

Sakamakon gwajin ya nuna nasara sosai, saboda bayan kwana uku kacal da cin abincin kabilar Hadza, sai ya samu karin bakteriyar da kashi 20 cikin 100, wanda hakan ke nuna ya samu karin lafiya matuka.

Bayanan hoto,

Mafarauta sai sun yi tafiyar kilomita da dama bayan sun kama nama, domin raba naman da aka kamo

Sai an shafe tsawon shekaru, kafin Farfesa Spector ya kammala bincikensa kan alfanin nau'in abincin da mutane ke ci a zamanin yanzu, amma cikin gaggawa ana neman masaniya kan irin abincin da kabilar Hadza ke ci, saboda al'amura sun fara sauya musu.

Shekara da shekaru manoma na ci gaba da mamaye filaye, har cikin yankunan al'ummar Hadza, kuma a shekara goma da ta gabata, sukan mamaye kadada 160 na filayensu duk shekara, inda suka yanke bishiyoyi da ciyayi domin shuka, da kuma bai wa shanu abinci. Lamarin da ya janyo korar namun daji iri-iri har 30 da kabilar Hadza suka shafe shekara dubu suna farautarsu a matsayin abinci.

Bayanan hoto,

Wani burgu kafin a babbaka shi a wuta

A ganina, abu mafi ban mamaki shi ne yadda manyan kamfanonin abinci suka iya riskarsu, 'yar tafiya ta minti 30 daga ramin bushiyar nan, sai ga wata bukka dauke da makunshin biskit da lemon kwalba, ana sayarwa.

Sai da na yi tafiyar sa'a tara a mota kirar Jeep kafin na gano yankin wannan al'umma, da na taras manyan kamfanonin duniya sun riga ni isowa.

Bayanan hoto,

Lemon kwalba ya kai ga yankin kabilar Hadza

Zigwadzee dai na daukaka al'adun al'ummar Hadza, wadanda ka iya janyo karewar namun daji kamar bushiya.

Mafarautan kabilar Hadza na taimakawa junansu, saboda suna da hadin kai da zumunci.

Ba su da wani jagora ko mai fada-a-ji tsakaninsu, kuma musammam a kan nama, babu wani tsari wajen rabo, ba kuma lallai ne kowa ya samu kashi daidai da na dan'uwansa ba.

Ana dafa kayan cikin naman dajin da aka kama ne kuma a cinye nan take, sannan a kai sauran naman sansanoni don rabawa.

A yayin da nake kallonsu, ina kuma dan gutsurar naman bushiya, sai na lura da wani abin sha'awa;

Farautar, da kuma abincin da nake ci, sun ba ni wata alaka da mutanen da.