Nigeria: 'Dole a rage yawan shekarun tsayawa takarar shugaban kasa'

Masu zanga-zanga na yin tattaki a titunan Abuja, babban birnin Najeriya, domin neman 'yan majalisar kasar su rage adadin shekaraun tsaya wa takarar shugaban kasa daga 40 zuwa 35.
Ana sa ran 'yan majalisar za su fara tattaunawa kan kudurin rage yawan shekarun tsayawa takarar a ranar Talata.
Batun na daya daga cikin batutuwan da za su tattauna a wani yunkuri na yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar.
Tuni dai maudu'in "#NotTooYoungToRun" wato ba kankantar shekaru a batun tsayawa takara, ya mamaye shafukan sada zumunta da muhawara na kasar.
Wannan zanga-zanga na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasar Muhammadu Buhari, mai shekara 74, ke fama da rashin lafiya.
Daya daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa BBC cewa dole ne a rage yawan shekarun domin a bai wa matasa dama su bayar da gudummawarsu.
Yawancin masu rike da madafun iko a Najeriya manya ne sosai.
Kuma kungiyoyin matasa sun dade suna korafin cewa ba a damawa da su a harkokin mulkin kasar.