Nigeria: Boko Haram ta sace masu bincike na NNPC goma

Mayakan Boko Haram

Asalin hoton, AP

Kamfanin mai na Najeriya ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai goma da suke masa aiki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

NNPC ya ce masana kimiyyar, wadanda wasunsu suka fito daga Jami'ar Maiduguri, sun shafe sama da shekara guda suna bincike kan abin da ya bayyana da tarin albarkatun mai a yankin Tafkin Chadi.

An yi awangaba da mutanen ne bayan wani kwantan bauna da aka yi musu a kusa da kauyen Jibi.

Mai magana da yawun NNPC Ndu Ughamadu ya ce mutanen sun "hada da malaman jami'a da direbobi da sauran ma'aikata".

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito mai magana da yawun Jami'ar Maiduguri yana cewa suna jiran karin bayani kan lamarin daga jami'an tsaro.

Sai dai ya tabbatar da cewa ma'aikatansu da suka yi tafi aikin bincike tare da jam'ian tsaro ba su dawo ba ranar Talata kamar yadda aka tsara.

Wasu rahotanni sun ce motoci goma ne ke cikin ayarin da masu binciken ke tafiya, amma daya ce kawai ta koma.

A baya-bayannan dai kungiyar Boko Haram ta masta da kai hare-hare, duk kuwa da ikirarin da hukumomin Najeriya ke yi na cewa sun karya kashin bayanta.

Akalla mutum 62 aka kashe a birnin Maiduguri da kewaye tun farkon watan Yuni. Sha-bakwai kuma sun rasa rayukansu a birnin a mako guda a wannan watan.

Ko a ranar Litinin ma wasu 'yan kunar bakin wake biyar sun kai hari wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu a Maiduguri, inda suka kashe mutum bakwai.

Rikicin Boko Haram ya kashe sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da wasu fiye miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.