Yawan maniyyin Turawa ya ragu

Sperm

Asalin hoton, JUERGEN BERGER/SCIENCE PHOTO LIBRARY

Wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa a kasa da shekara 40, yawan maniyyin da maza ke da shi ya ragu da sama da rabi a kasashen Turawa na yammacin duniya.

Masana kimiyya sun wallafa sakamakon nazari daban-daban har 185 na yawan maniyyin mutane daga 1973 zuwa 2011.

Masanan sun gano cewa raguwar ba za ta iya kasancewa saboda bambancin yawan al'umma ba ne ko kuma bambancin hanyoyin binciken da aka yi amfani da su ba.

Daya daga cikin masu binciken, Dr Hagai Levine, na jami'ar Hebrew University ta Birnin Kudus, ya ce abin da aka gano, wata zaburauwa ce da ya kamata a gaggauta daukar mataki a kai, idan aka yi la'akari da muhimmancin yawan maniyyi ga maza wajen haihuwa da kuma rayuwar dan'adam.