Nigeria: Rikicin kabilanci ya sa an tura jirgin yaki Taraba

Sojojin za su taimakawa dakarun kasa

Asalin hoton, Nigerian Air Force

Bayanan hoto,

Jirgin sojin zai je daniyyar taimakawa dakarun kasa

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta tura wani jirgin saman yakinta jihar Taraba da zummar dawo da zaman lafiya.

Wata sanarwa da ta fitar ta ce "ta tura daya daga cikin jirage masu saukar ungulu karamar hukumar Takum da ke jihar domin tallafawa dakarun da ke kasa a yunkurin tabbatar da tsaro a yankin".

A cewar sanarwar, aikawa da jirgin zai hana bangarorin da ke fada da juna sake gwabzawa.

Ta kara da cewa jirgin ya soma shawagi a yankin Mambilla da zummar wanzar da tsaro.

Daruruwan mutane ne ake fargabar sun mutu a tashin hankalin da ya barke a makon jiya tsakanin Fulani da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna a kwanakin baya.

Fulanin sun zargi gwamnatin jihar da hada baki da Mambillawa wurin far musu da yaki, zargin da gwamnatin ta musanta.

Sai dai babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ke kula da jihar ta Taraba, ya bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a matsayin "kisan-kare-dangi".

Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a fadar Sarkin Mambila da ke jihar ta Taraba yayin wani taro da shugabannin al'ummomin yankin.

Ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila.

A cewarsa, "An yanka kananan yara 'yan shekara biyu, an kashe mata masu ciki; abin da aka yi musu ya fi abin da 'yan Boko Haram ke yi, domin 'yan Boko Haram ba sa kashe kananan yara. Niyya aka yi ta yi musu kisan-kare-dangi".

Rundunar sojin saman ta ce nan gaba kadan za ta tura jirgi mai saukar ungulu Kafanchan da ke jihar Kaduna domin tallafawa dakarun kasa da ke yankin.

Shi ma wannan jirgin za a tura shi ne a wani mataki na samar da zaman lafiya a kudancin Kaduna.