Jamhuriyar Niger: 'Karin kudin awon kaya zai fi shafar talaka'

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Wani kudiri da ma'aikatar Custom ko Douane da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka fitar kan karin kudi ga kayayakin 'yan kasuwa na awo, ya hadassa bacin rai ga yan kasuwa.

A cewar 'yan kasuwan dai halin da ake ciki ba lokaci bane na karin kudi, kasancewar kudaden kayayakin masarufi ne zasu kara tsada.

Tun a shekara ta 1994 ne kasar ta Jamhuriyar Nijar din ta rattaba hannu kan yarjejeniyar nan ta kungiyar cinikayya ta duniya-- dokar da ta kamata a ce kasar ta fara amfani da ita tun a shekara ta 1999, shekaru biyar bayan yarjejeniyar.

Sai bayan shekaru 18 ne bayan wannan yarjejeniya ne dai Nijar din ta yi alwashin fara amfani da ita.

A wata sanarwa ce dai hukumar kula da shige da ficen kaya ta Kwastan ko kuma Douane ta sanar da karin kudi kan dukkan kayyaki na shige da ficen.

Wani jami'in hukumar ta Doaune din ya shaida wa BBC cewa yanzu an saka wani tsarin da ake aiki da shi a fadin duniya.

'' Wannan tsari shine daidai kudin da mutum ya biya na kayanshi ya kawo su ofishin Douane din, sune aka ce ya biya kudin haraji daidai da su.''

Jami'an ya kara da cewa ya kamara jama'a su yi aiki da doka, wacce ta tanadi cewa da zarar kayyaki sun kai watanni hudu mai su bai je ya biya kudin fito ya karba ba, za su yi gwanjon su.

Shugaban kungiyar kwadago ta masu shiga da fita da kaya ta Nijar din, Alhaji Sani Shekarau ya ce da wannan doka talaka ne kawai zai tagayyara, saboda farashin kayayyaki za su yi tashin gwauron zabi.

'' Abin dala goma idan ya koma dala ashirin,wadanda kawai za su ji dadi sai masu hali, amma talaka ne zai dandana kudarsa,'' in ji Sani shekarau din.

Ya kuma ce hukumomi ba su shawarce su ba, sai kawai suka ga takardar sanarwa.

Yanzu haka dai 'yan kasar ta Jamhuriyar Nijar din da dama ne ke fama da matsin tattalin arziki, talauci da kuma fatara.