An nemi Falasdinawa da su ci gaba da kaurace wa Al-aqsa

Asalin hoton, Getty Images
Falasdinawan dai sun rika sallah a waje don nuna rashin amincewa da saka shingayen.
Hukumar gudanarwar masallacin Bait-al-mukaddas ta bukaci masallata da su ci gaba a kaurace wa haramin duk da cewa Isra'ila ta ciccire shingayen tsaron da ta kafa da suka jawo takaddama.
Hukumar wadda aka fi sani da Waqf Foundation ta ce kada kowa ya shiga masallaci har sai wani kwamitinta na kwararru ya kammala wani aikin dudduba sauye-sauyen da aka yi wa ma sa.
An ciccire na'urorin ne cikin daren Talata sakamakon amincewa da cire su da majalisar tsaron gwamnatin Isra'ila ta yi.
An saka su ne kusan makonni biyun da suka gabata bayan wani ya bindige 'yansandan Isra'ila biyu lokacin suke tsaron masallacin.
Falasdinawa dai sun ki yarda su bi ta cikin na'urorin su shiga masallacin saboda fargabar kada su bayar da kafar sauya wata dadaddiyar yarjejeniya kan shigarsu masallacin.