Nigeria: Osinbajo ya rantsar da sabbin ministoci

Osinbajo new ministers

Asalin hoton, Twitter/@profOsinbajo

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na farko Yemi Osinbajo ya rantsar da masu manyan mukamai tun da ya fara tafiyar da al'amuran kasar

Mukaddashin Shugaban Nigeria Yemi Osinbajo ya rantsar da sabbin ministocin nan biyu da suka kwashe fiye da wata biyu suna dakon shan rantsuwar da safiyar Larabar nan.

An rantsar da sabbin ministocin ne a lokacin zaman majalisar zartarwa na kasar a ranar Laraba da safe.

A kwanakin baya ne majalisar dattawan kasar ta amince da Stephen Ocheni daga jihar Kogi da Sulaiman Hassan daga jihar Gombe.

Sai dai rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari da tafiyarsa jinya Ingila ta sa an jinkirta rantsar da su.

Kuma hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar kasar.

Mista Ocheni ya maye gurbin tsohon Ministan Kwadago marigayi James Ocholi wanda ya rasu cikin wani hadarin mota a bara.

Yayin da Sulaiman Hassan ya maye gurbin tsohuwar Ministar Muhalli Amina Muhammad wadda aka nada mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.