Nigeria: Arzikin Aliko Dangote 'ya ragu'

Aliko Dangote tare da 'yarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aliko Dangote ya dade yana shiga cikin jerin attajiran dduniya da Forbes ke wallafawa

Hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya yi kasa a jerin masu kudin duniya inda ya fado daga mataki na 51 zuwa 105, in ji mujallar Forbes.

Mujallar ta ce arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 15.4 a shekarar 2016 zuwa biliyan 12.2 a bana.

Hakan dai ya faru ne, a cewar Forbes, saboda faduwar darajar kudin Najeriya.

Alhaji Dangote, wanda ya fi karfi a harkar siminti da sukari da filawa, ya ja hankalin duniya lokacin da ya ce yana son sayen kulob din Arsenal cikin shekara hudu masu zuwa.

A ranar Alhamis ne, Shugaban kamfanin Amazon Jeff Bezos ya maye gurbin Bill Gates na wani dan lokaci a matsayin mutumin da ya fi kowa arziki a duniya.

Sai dai ba a jima ba ya koma mataki na biyu, inda mutumin da ya kirkiro kamfanin Microsoft din ya koma kan matsayinsa.