Nigeria: Boko Haram ta sako ma'aikatan NNPC

Mayakan Boko Haram

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuar sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya tabbatar da kubutar da wasu daga cikin ma'aikata goman da ya dauki nauyinsu zuwa binciken mai a yankin Tafkin Chadi.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da sace masanan, wadanda wasunsu suka fito daga Jami'ar Maiduguri.

Rundunar sojin kasar kuma ta ce dakarunta suna can suna farautar mayakan na Boko Haram.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka ya shaida wa BBC cewa dakarunsu sun yi nasarar kubutar da wasu, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu.

Sai dai bai fadi adadin wadanda aka kubutar ba, ko kuma wadanda suka mutu.

Shi ma kakakin kamfanin NNPC, Ndu Ughamadu ya ce an kubutar da uku daga cikin jami'an safiyo da masu nazarin halittun karkashin kasa da aka sacen.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato rundunar sojin Najeriya na cewa ta gano gawar ma'aikatan tara tare da ta farar hula daya da ke tare da su.

NNPC ya ce masu nazarin halittun karkashin kasar sun shafe sama da shekara guda suna bincike kan abin da ya bayyana da tarin albarkatun mai a yankin Tafkin Chadi.

An yi awangaba da mutanen ne bayan wani kwantan bauna da aka yi musu a kusa da kauyen Jibi.

Mista Ndu Ughamadu ya ce mutanen sun "hada da malaman jami'a da direbobi da sauran ma'aikata".

A baya-bayannan dai kungiyar Boko Haram ta matsa da kai hare-hare, duk kuwa da ikirarin da hukumomin Najeriya ke yi na cewa sun karya kashin bayanta.

Akalla mutum 62 aka kashe a birnin Maiduguri da kewaye tun farkon watan Yuni. Sha-bakwai kuma sun rasa rayukansu a birnin a mako guda a wannan watan.

Ko a ranar Litinin ma wasu 'yan kunar bakin wake biyar sun kai hari wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu a Maiduguri, inda suka kashe mutum bakwai.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuar sama da mutum 30,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da wasu fiye miliyan biyu suka tsere daga gidajensu.