Nigeria: Majalisa tana neman rage karfin shugaban kasa

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An samu takun saka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa a kwanakin baya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kuduri da ke neman rage karfin shugaban kasar wajen tsarawa da kuma amincewa da doka.

'Yan majalisar sun amince a ragewa shugaban kasar karfin ikonsa na hawa kujerar na ki kan kudurin dokokin da majalisar ke tsarawa, a wani bangare na gyaran da suke yi wa tsarin mulkin kasar.

Masu sharhi na ganin majalisar na kokarin rage ikon da shugaban kasa ya ke da shi da kuma mayar da shi hannunta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin bangaren zartarwa da kuma na majalisa kan wasu batun nadin mukamai.

Majalisar ta kuma amince da kudurin da ke neman gindaya lokaci mafi kankanta da shugaban kasar zai mika sunayen ministocin da zai nada ga majalisar.

Har wa ya daya daga cikin kudurorin ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Haka zalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar dokokin kasar.

'Yan majalisar sun kuma amince da dan takara mai zaman kansa.

A ranar Talata ne dai matasa suka yi gangami a kan titunan Abuja, babban birnin kasar, domin yin tur da yunkurin watsi da kudurin, kuma suka yi ta tafka muhara a shafukan sada zumunta kan maudu'in #NotTooYoungToRun wato babu wanda ya yi kankanta wurin tsayawa takara.

Mambobi 86 daga cikin 'yan majalisar sun amince da kudurin gyara tsarin mulkin yayin da 10 daga ciki suka ki amince wa da shi kuma dan majalisa daya ya ki kada kuri'a.