Nigeria: Za mu yi wa jihohi zamiyar kudaden bashi

Kudin Nijeriya

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Hukumar tarawa da rabon arzikin Nijeriya ta ce tana bin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi basussukan kudade da dama

Hukumar tarawa da rabon arzikin kasa ta Nijeriya, ta bayyana aniyar zame basussukan da suka taru a kan jihohi da kananan hukumomi, da kuma wasu ma'aikatu da hukumomi na gwamnatin.

Ta ce ya kamata a ce jihohin sun shigar da kudaden a asusun rabon arzikin kasa, amma sun gaza yin hakan.

Kudin dai kimanin Naira biliyan 115, sun hada da harajin da jihohin da ma'aikatun suka karba amma suka kasa zubawa a asusun tarayya tsawon kimanin shekara 10.

Malam Hassan Mahe Abubakar, daraktan kula da kudaden shiga da ba na man fetur ba na hukumar, ya shaida wa BBC cewa wannan haraji na daya daga cikin hayoyin samun kudin shiga.

Ya ce wadannan kudade su ne ake tattarawa duk wata ana rarrabawa tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi.

''Kudaden da kasar ke samu daga bangaren albarkatun man fetur yanzu al'amura sun ja baya'', don haka biyan wadannan basussuka na da matukar muhimmancin'', in ji Malam Mahe.

Hukumar dai ta ce akwai jihohin da har yanzu suka ki amincewa su tattauna da jami'an hukumar da suke zagaya wa, domin tabbatar da kididdigar da aka ba ta.

Sai dai a wasu lokuta gwamnatocin jihohin da kananan hukumomi kan koka da rashin biyan su kudaden da suka yi wasu ayyukan gwamnatin tarayya a jihohin su.