BH: An umarci jami'an tsaron Nigeria su koma Maiduguri

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare duk da ikirarin soji na murkushe su

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare duk da ikirarin soji na murkushe su

Mukaddashin shugaban Najeriya ya umarci manyan hafsan sojojin kasar da su tattara su koma Maiduguri, cibiyar Boko Haram.

Yemi Osinbajo ya bayar da umarnin ne bayan da mayakan kungiyar suka kashe sama da mutum 40 a wani harin kwantan-bauna da suka kai wa tawagar masu binciken mai na kamfanin NNPC.

Ministan tsaron Najeriya ya ce za a sayi karin kayan aiki na zamani wadanda za su bai wa jami'an tsaro damar ganin abokan gaba daga nesa.

Mafi yawancin mutanen da aka kashe a harin na ranar Talata a jihar Borno sojoji ne da 'yan sintiri ko kuma 'yan kato da gora.

Yawancin masana kimiyyar sun fito ne daga jami'ar Maiduguri, inda wani malami ya shaida wa BBC cewa an kashe biyar daga cikin ma'aikatansu, yayin da ba a ji duriyar wasu guda hudu ba.

Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da jami'an sojin kasar, Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali ya ce jami'an tsaro na fuskantar matsala wurin tunkarar mayakan a lokacin damuna.

Sai dai ya kara da cewa jama'a su kwantar da hankalinsu domin matakin da za a dauka "zai kawo karshen irin wadannan hare-hare".

Tun da farko dai jami'an tsaro sun ce sojoji tara ne suka mutu a kokarin ceto mutanen da aka sace din .

Wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubakar wanda ya ziyarci dakin ajiyar gawa na asibitin jami'ar Maiduguri, ya ce ya ga gawarwakin mutane duk sun rube.

Ya ce "Biyar na 'yan kato da gora ne a inda kuma ta shidan ta soja ce."

A bangare guda kuma, Ministan man fetir na kasar Dr Ibe Kacikwu ya sanar da dakatar da ci gaba da neman mai a yankin.