Boko Haram: 'Mutum fiye da 40 aka kashe a harin Borno'

Sojojin Najeriya
Bayanan hoto,

Mafi yawan wadanda aka kashe sojoji ne da 'yan sintiri

Wasu wadanda suka ga gawar mutanen da suka mutu a harin da Boko Haram ta kai wa tawagar masu aikin binciken mai a jihar Borno ranar Talata sun shaida wa BBC cewa wadanda suka mutu sun haura 40.

Ma fi yawancin mutanen da aka kashe din sojoji ne da 'yan sintiri ko kuma kato da gora.

Tun da farko dai sojojin kasar sun ce sojojin tara suka mutu a kokarin ceto ma'aikatan wadanda da yawancinsu ma'aikatan jami'ar Maiduguri ne.

Wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubakar wanda shi ma ya ziyarci dakin ajiyar gawar, a inda ya ce ya ga gawarwakin mutane duk sun rube.

Ya ce "Biyar na 'yan kato da gora ne a inda kuma ta shidan ta soja ce."

A ranar Talatar ne dai kungiyar ta Boko Haram ta abka wa wata tawagar ma'aikatan aikin hakar man fetir da ke tafe cikin rakiyar sojoji da 'yan sintiri.

Yawancin ma'aikatan sun fito daga jami'ar Maidguri ne.

Yanzu haka karamin ministan man fetir na Najeriya, Dr. Ibe Kacikwu ya sanar da dakatar da ci gaba da neman mai a yankin.