Kun san shugabannin da aka sauke don cin hanci?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Akwai babban darasin da za a koya – Auwal Rafsanjani
  • Akwai cikakkiyar tattaunawa da mai fafutikar kare hakkin dan Adam, Auwal Musa Rafsanjani, game da darasin da za a koya daga sauke Mista Sharif, sai ku latsa alamar lasikifa da ke sama don sauraro.

Yayin da kotun kolin Pakistan ta sauke Fira Ministan kasar Nawaz Sherif, BBC ta yi nazari kan wasu shugabanni da suka sauka daga kujerunsu biyo bayan zargin cin hanci da rashawa.

1. Fira Minista Nawaz Sharif: Ya kasance Fira Ministan Pakistan daga ranar 5 ga watan Yuni 2013 zuwa 28 ga watan Yulin 2017.

Nawaz Sharif ya yi murabus ne bayan alkalin kotun kolin Pakistan ya sauke shi daga mukaminsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nwaz Sharif ne shugaban kasa na baya-bayan nan da aka cire a kan kujerarsa bayan zargin cin hanci da rashawa ba tare da amfani karfin soja ba

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa sakamakon abin kunyar nan na Panama Papers ya gano cewa yana da dukiya a kasashen da ke kaucewa biyan haraji.

Mista Sharif ya sha musanta aikata ba daidai ba a kan wannan batu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana ci gaba da shari'ar Ms Park Geun-hye

2. Shugaba Park Geun-hye: Ita ma Shugaba Park Geun-hye ta Koriya ta Kudu ta yi mulkin kasar daga ranar 25 ga watan Fabrairu na shekarar 2013 zuwa ranar 10 ga Maris na shekarar 2017.

Majalisar dokokin kasar ce tsige Geun-hye bisa zarge-zargen da suka hada da cin hanci da rashawa.

Baya ga haka ne aka gurfanar da shugabar tare da aminiyarta, Choi Soon-Sil, gaban kotu kan zargin cin hanci da rashawa.

Sai dai shugabar da aminiyarta sun musanta zargin da aka yi musu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dokokin Brazil ce ta tsige Dilam Rouseff bisa zargin yin ba daidai ba game da kasafin kudin kasar

3. Dilma Rouseff: Shugaba Dilma Vana Rouseff ta shugabanci Brazil ne daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2011 zuwa ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2016.

Majalisar dokokin Brazil ta kada kuri'ar tsige Shugaba Dilma Rousseff ne sakamakon zargin da aka yi mata na aikata almundahana a kasafin kudin kasar.

Matakin ya kawo karshen shekara 13 da jam'iyyarta ta Workers Party ta yi a kan mulki a kasar Brazil.

Rousseff ta musanta zargin da aka yi mata.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Perez ya kwashe shekara biyar yana mulkin kasar Guatemala

4. Otto Perez Molina: Shugaba Otto Perez Molina ya shugabanci kasar Guatemala ne daga ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2012 zuwa 3 ga watan Satumbar shekarar 2015.

Shugaba Perez ya yi murabus ne bayan masu gabatar da kara sun yi zargin cewa shugaban ya shirya damfarar hukumar hana fasakwaurin kasar kan miliyoyin daloli.

Majalisar dokokin kasar ta cire masa kariyar da yake da shi daga gurfana a gaban kuliya.

Wani mai magana da yawun shugaban ya ce shugaban ya yi murabus ne domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da ake masa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Paksas bai cika shekara biyu a kan mulki ba aka tumbuke shi

5. Rolandas Paksas: Shugaba Rolandas Paksas ya shugabanci kasar Lithuania ne daga shekarun 2003 zuwa 2004.

An cire Mista Paksas daga mulki ne bayan kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa shugaban kasar ya yi amfani da mukaminsa ta yadda bai dace ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a tabbatar da zarge-zargen da majalisar dokoki ta dogara da su ba wajen tsige Abdurrahman Wahid

6.Abdurrahman Wahid: Shugaba Abdurrahman Wahid ya shugabanci kasar Indonesia daga ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 1999 zuwa ranar 23 ga watan Yulin shekarar 2001.

Majalisar dokokin kasar ce ta tsige shi kan zargin cin hanci da rashawa, zargin da ba a tabbatar ba tukuna.

Nigeria: Yaki da cin hanci ya fara a bangaren Shari'a

Buhari zai iya yaƙi da cin hanci a cikin gidansa?

Nigeria: Cin hanci na dakile yaki da Boko Haram—TI

7. Fernando Collor de Mello: Shugaba Fernando Collor de Mello ya shugabanci Brazil ne daga shekarar 1990 zuwa 1992.

Ya yi murabus ne a lokacin da majalisar dokokin kasar take fara zaman tsige shi da kuma yi masa shari'a kan zargin cin hanci da rashawa.

Bayan ya yi murabus, majalisar ta ci gaba da zaman kuma ta same shi da laifi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sepp Blatter ya dade yana shugabancin hukumar FIFA

8. Sepp Blatter: Sepp Blatter ya shugabanci hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) daga ranar 8 ga watan Yunin shekara 1998 zuwa 21 ga watan Disambar shekarar 2015.

Kwamitin da'a na hukumar ne ya dakatar da Blatter tare da hana shi yin wani abu da ya shafi kwallon kafa har tsawon shekara takwas.

Labarai masu alaka