Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu kayatattun hotuna daga sassan nahiyar Afirka daban-daban da kuma na wasu sassan duniya a makon jiya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yar wasan tennis daga Najeriya Adetayo Adetunji wadda tauraruwarta take haskawa ta doke takwararta Zeel Desai ta Indiya ranar Jumaa'a a gasar matasan kasashen renon Ingila da ake yi a kasar Bahamas. 'Yar wasan mai shekara 18 ta doke abokiyar karawarta ta Ghana Miriam Ibrahim a zagaye na biyu, sai dai daga baya ta fita a lokacin da ta kai matakin kusa da karshe.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani wurin gyaran mota a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, an baje-kolin kayayyakin motoci domin sayarwa a wajen wurin ranar Litinin. Kasuwanci dai na habaka a kasar tun bayan da dakarun kungiyar kasashen Afirka da sojojin gwamnati suka fitar da mayakan sa-kai daga yankin.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu masunta a kogin Nilu na birnin Alqahira a kasar Masar, suke kamun kifi ranar Juma'a.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai goyon bayan jam'iyya mai mulki a kasar Kenya (Jubilee Party) ya sanya hoton fuskar Shugaba Uhuru Kenyata ya yin yakin neman zabe a Nairobi ranar Juma'a - ranar 8 ga watan Agusta ne za a yi babban zabe a kasar.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadansu mutane suna tafiya kusa da wani bango da wani mai zane-zane Solomon Muyundo ya yi rubutu kan bukatar wanzar da zaman lafiya a wata unguwa da Nairobi a kasar Kenya ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadansu magoya bayan kasar Kongo suna rera taken kasar a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny, a Abidjan babban birnin Ivory Coast ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masassaki, Kaba Abdoulaye na kasar Guinea, yana sassaka gunki a birnin Abidjan, inda yake sa ran sayar wa masu sha'awar wasanni da suka kawo ziyara kasar ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mai dakinsa Aisha Buhari (daga dama), da mai dakin gwamnan jihar Benue (daga hagu) a Landan, a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnoni a gidan da yake jinya wato Abuja House ranar Laraba, inda yake jinya karo na biyu a bana.

Labarai masu alaka

Labaran BBC