Ra'ayi: Ko rage shekarun 'yan takara zai ba matasa dama a Najeriya?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Ko rage shekarun 'yan takara zai ba matasa dama a Najeriya?

Ga alama hankoron matasan Najeriya na ganin an rage shekarun takarar mukaman siyasa a kasar, domin a rika damawa da su, na gab da biyan bukata. Yanzu haka dai majalisun kasa sun amince a yi sauyi ga sassan kundin tsarin mulkin kasar da ya shafi wannan batu. Matasan dai na zargin tsaffin 'yan siyasa da mayar da su 'yan kallo. To shin rage yawan shekarun ne zai kai su ga samun madafun iko ko kuwa akwai wani abu daban? Batun da aka tattauna a kan shi kenan a filin Ra'ayi Riga.