Ujajjkajajjajajnha hahahjha
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda kayan lefe ke kawo wa aure cikas

  • Akwai ci gaban cikakkiyar zantawar da Fatima Zarah Umar ta fara da wasu mutane game da tasirin kayan lefe, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Daya daga cikin manyan batutuwan da suke tasowa game da batun aure a kasar Hausa shi ne kayan lefe.

Idan ana maganar lefe kowa ya san cewa batu ne na kudi musamman idan aka yi la'akari da gidan da amaryar ta fito.

Shin ta fito daga gidan masu hali ne ko kuwa 'yan rabbana ka wadata mu.

Ta fito daga birnin ne ko kauye? Da kuma yadda 'yan uwanta za su rika tambaya cewa akwati nawa aka kawo?

Wadannan kayayyaki aka sanya a akwatin? Manyan atamfofi nawa ne a ciki? Akwai atamfa Super ko Java?

Wadanne irin gyale aka sa a akwatin kuma ko kayan sun burge surukan angon?

Yadda na fahimci abin shi ne kayan lefe wani abu ne da ya yi kama da kyauta amma ba wani abu ba ne da wajibi ya burge mutum. Ba wata dama ce ta bayyana yawan arzikin mutum ba.

Aure bai dogara kacokan a kan lefe ba.

Ko miji da gidansu sun yi lefe, ko ba su yi ba, nauyin samar wa mace tufafi ya rataya ne a wuyan mijinta.

Yadda muka ba lefe muhimmanci abin kamar ita amarya ba za ta kara sanya wasu kayan ba idan ba na lefe ba duk tsawon rayuwarta.

A wasu lokuta iyaye ba sa tambaya kan yadda ko ya dace a saye irin wadannan kayayyaki.

Yana da wuya ka ga wani yana tambaya game da yadda lefe zai amfani zamantakewar aure.

Mene ne amfanin kayan lefe a aure?

Ko wajibi ne sai an yi kayan lefe? Yana da wani tasiri wajen zamantakewa? Ko idan aka yi wa amarya akwatuna da dama na samar da kyakkyawan zaman aure?

Wane ne yake cin moriyar kayan lefe? Bayan mutanen da suke yada tsegumi da kananan maganganu?

A duk lokacin da na ga samari suna kokorin hada kayan lefe, nakan tausaya musu.

Bai kamata aure ya zama kamar wani cinikin kasuwanci ba. Aure ana so ne ya kasance har abada.

Ko al'umma za su daina damuwa da lefe da kayan daki, don su mayar da hankali kan kyawawan dabi'u da kuma tarbiyya?

Ina tausayawa 'yan uwana wadanda suka fito daga yankin arewa-maso-gabashin Najeriya saboda hada kayan lefe a wannan yanayi na matsin tattalin arziki ba abu ba ne mai sauki.

Sai dai komai ya yi tsanani maganinsa Allah.

Har ila yau, ina tausayawa iyaye wadanda suke hada wa 'ya'yansu kayan daki saboda yadda hakan yake cin makudan kudi.

Ya kamata ne kowannenmu ya sauke nauyin da ke wuyansa.

Mata da dama sun shaida min cewa bayan da aka yi musu lefe, mazajensu ba su damuwa wajen tufatar da su.

Lefe ba ya dauke nauyin tufatarwa da ya rataya a wuyan mai gida.

Mata da dama sun san cewa ana fara rikici ne da zarar dara ta fara karewa.

Wacce irin al'umma muke ciki wadda iyayen amarya suke yi wa ango kusan komai - ciki har da dara wadda takan kai tsawon kimanin shekara guda bayan aure, amma abin mamakin shi ne yadda har yanzu ake kara samun yawaitar mutuwar aure.