Mutum biyu sun mutu a filin wasan Afirka ta Kudu

Filin wasa Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka ji raunuka a wani turmutsitsi filin wasan kwallon kafa na kasar Afirka ta Kudu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana.

Al'amarin ya faru ne a wani filin wasa da ke birnin Johannesburg yayin da ake wasa tsakanin kungiyoyi biyu wato Kaizer Chiefs da Orlando Pirates.

Sai dai ba a san abin da ya jawo turmutsitsin ba tukuna a filin wasan wanda ke daukar 'yan kallo kimanin dubu 87.

Afirka ta Kudu ta kori kocinta Mashaba

Afirka ta Kudu: Zuma ya shiga tsaka mai wuya

Labarai masu alaka