An fara jigilar alhazai a Nigeria

Wasu maniyya da za su ta daga shiyyar Abuja Hakkin mallakar hoto WHATSAPP
Image caption Akwai kimanin alhazai dubu 60 da za su je Kasa-Mai-Tsarki don sauke farali a bana

Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta ce ta fara jigilar maniyya aikin hajjin bana a Najeriya inda alhazai suka fara tashi daga shiyyar Abuja ranar Lahadi.

Shugaban hukumar Abdullahi Muktar ya shaida wa BBC cewa "an yi sahun farko daga Abuja inda aka kwashe alhazai 480 da misalin karfe 3:16 na ranar Lahadi."

Ya ce ana saran kammala jigilar mahajjatan kasar a ranar 20 ga watan Agusta.

Akwai kimanin alhazai dubu 60 da za su je Kasa-Mai-Tsarki don sauke farali a bana, kamar yadda ya ce.

"Adadin zai iya karuwa saboda yadda har yanzu ake ci gaba da karasa biyan kudin a jihohin kasar.

"Don haka har yanzu kofa a bude take ga duk wanda bai kammala biyan kudinsa ba, zai iya karasawa yanzu," in ji shi.

Labarai masu alaka