NNPC: Muna tare da ma'aikatan Jami'ar Maiduguri

Kanti Baru Hakkin mallakar hoto NNPC Facebook
Image caption Ma'aikatan jami'ar Maiduguri da na kamfanin NNPC na aiki ne don gano albarkatun mai a yankin tafkin Chadi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya ce zai yi duk abin da zai iya don ganin ya tallafa wa Jami'ar Maiduguri da iyalan mutanen da mayakan Boko Haram suka sace a makon da ya gabata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ndu Ughamadu, ya fitar ta ambato babban jami'i mai kula da sashen ayyukan iskar gas da makamashi na kamfanin NNPC Injiniya Sa'idu Mohammed, yayin ziyarar da ya kai a karshen makon jiya, na cewa sun kasance manyan abokan aiki da jami'ar Maiduguri tsawon shekaru.

Ya kara da cewa, kuma tabbas duk lokacin da al'amari irin wannan ya faru, a cikin irin wannan hali, ba za su gudu su bar abokansu ba.

Sanarwar ta ambato shugaban jami'ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi na alkawarta ci gaba da aiki da kamfanin NNPC wajen binciken makamashin da ke jibge a yankin tafkin Chadi duk da harin baya-bayan nan na 'yan ta-da-kayar-baya da ya ritsa da ma'aikatan jami'arsa.

A cikin makon jiya ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kubutar da ma'aikatan binciken, kafin daga bisani ta nemi afuwa kan abin da ta ce kuskure a bayanan da ta bayar.

Ta ce ya zuwa lokacin dakarunta sun gano karin gawawwakin soja biyar, da 'yan kato da gora su 11 da kuma gawawwakin jami'an binciken man fetur guda biyar.

Sanarwa ta ci gaba da cewa ba a ji duriyar "mutum shida cikin ma'aikata 12 da suka fita aikin binciken ba, amma ma'aikacin kamfanin NNPC 1 ya kubuta, in ji ta.

Tuni dai mukaddashin shugaban Nijeriya, Yemi Osinbajo ya bukaci dakarun sojin kasar su ceto ragowar ma'aikatan binciken da aka sace, bayan an ga wasu uku a hoton bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar.

Bangare guda kuma, babban hafsan sojin Najeriyar, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya umarci kwamandan rundunonin da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, Manjo Janar Ibrahim Attahiru da ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Hafsan sojin ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya aike wa manema labarai, inda ya kara da cewa an bai wa kwamandan kwanaki 40 kacal ya kawo jagoran kungiyar ta Boko Haram.

A halin da ake ciki dai, sojojin sun yi kwana tara cikin 40 din da aka deba musu na gudanar da wannan aikin.

Kuma 'yan Najeriya sun zuba ido dan ganin ko hakan mai yiwuwa ce, ganin ko a farkon hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulki, ya bai wa sojojin kasar wa'adin watanni bakwai su kawo karshen kungiyar Boko Haram amma har yanzu ba a kai ga nasarar murkushe su ba.

Labarai masu alaka