Kun san wanda ya mari matarsa don ta fadi sunansa a karon farko?

Women practise saying their husband's names

Miliyoyin mata a kasar Indiya ba su taba fadar sunayen mazajensu ba, wannan wata hanya ce ta nuna da'a da biyayya ga mazajen. Sai dai kuma a halin da ake ciki masu fafutuka na kokarin sauya wannan dabi'a ta hanyar sanya matan fadin sunan miji a karo na farko.

Wannan al'ada dai an fi yinta a yankunan karkara, duk da cewa ana samun kalilan daga cikin matan birane da ke amfani da al'adar. Amma yanzu wasu masu fafutuka na kokarin sauya matan karkara ta hanyar sanya su fadar sunan miji a karon farko.

Abin tambayar shi ne me ye a cikin sunan?

Idan har ke 'yar Indiya ce, kuma mutumin da ake maganar sunansa a kai ya kasance mijinki ne akwai tarin kalubale wajen fadar sunansa. Na kuma gane hakan ne tun ina karama.

Iyayena sun yi aure shekara 73 da ta wuce, amma a bara mahaifina ya rasu. A lokacin da suka yi aure, mahaifiyata ba ta kai shekara 11 ba, mahaifina kuma 15.

Tun da suka yi aure, suna zaune ne a wani dan karamin kauye da ke arewacin jihar Uttar Paradesh, daga bisani kuma ya zama Kolkata, tsawon lokacin da suka yi tare ba ta taba kiransa da sunansa ba.

A duk lokacin da take magana da mu 'ya'yanta ba ta taba fadar sunan babanmu sai dai ta ce ''babuji'' - da harshen Hindu hakan na nufin ''uba''. Sannan a duk lokacin da take magana da shi sai dai ta ce ''Hey ho'', hakan na nufin ''Ji mana''.

A lokacin da muka fara girma, muka kuma fahimci abin da ta ke nufi ko da yaushe muna tsokanarta da yin dariya kan yadda ta ke kiran babanmu. Akwai lokacin da muka shirya mata gadar zare don dai ta fadi sunansa ko da sau daya ne, amma sam ta ki fada.

Haka sauran matan da ke gidanmu kai har da makwabta, sam ba sa fadar sunan mazajensu. Haka ya ke ga miliyoyin mata a kasar Indiya ba sa fadar sunan mazajensu, abin kuma babu ruwansa da banbancin addini ko al'ada ko shiyyar da ka fito.

Hakan bai rasa nasaba da yadda aka dauki miji kamar wani Ubangiji a kasar Indiya, kuma yarinya tun tana karama ake dorata kan tarbiyyar girmama miji.

A kan fadawa mace idan tana fadar sunan mijinta, wani bala'i zai iya fada mata sannan shi kansa mijin ba zai yi tsawon rai ba. Ba sunansa ne kadai ya haramta mace ta saya ba, har da sunan surukanta. Kuma idan har ta fadi sunansa, hakan yana nufin ta gayyato bala'i da musiba ga iyalanta.

Akwai wata mace da ta fito daga yammacin jihar Orissa, da ta gamu da fushi da Allah-wadai saboda fadar sunan mijinta da ta yi.

Wata mace mai suna Malati Mahato, ta shaidawa masu shirya fina-finan sa kai na wata kungiya mai fafutukar ganin an sauya dabi'ar sakaya sunan miji cewa: ''Wata rana, kanwar mijina ta tambayi wa ye zaune a wajen gida, sai na fada mata sunayen mazajen da ke wajen ciki har da sunan kawun mijina''.

Hakkin mallakar hoto Video Volunteers

Ai kuwa sai kanwar mijin ta kai kararta wajen dagacin garinsu, ai babu bata lokaci aka kore ta daga kauyen baki daya, har da 'ya'yanta aka kai su can wani kebantattacen wuri a kauyen da ake kai mutanen da suke aikata babban zunubi, kuma mutane su kai mata tofin Allah-tsine. Ta kwashe wata 18 ita da 'ya'yanta a wurin.

Farfesa A R Vasavi, daya daga cikin masu fafutukar kawo karshen al'adar ko rage ta ya yi karin haske kan yadda ake kallon mijin aure a al'adar kasar Indiya.

"Ka san a Indiya ana kallon miji kamar wani Ubangiji, dan haka dole a bauta masa. Sannan al'ada ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hakan, ana kallonsa a matsayin wanda iyalai suka dogara da shi, wajen ciyarwa da tufatarwa da dauke dukkan lalurorin iyali.

Shi ne mai karfin fada aji a cikin iyali, dole abi shi a kuma yi masa biyayya''.


Sunayen da mata a Indiya suke kiran mazajensu ba tare da sun ambaci sunansa ba

  • Mata kan kira mazajensu da sunan ''Uba'', ko su kira shi da sunan ''Baban wane/wance'' a cikin 'ya'yansa, su kan kuma kira shi da aikin da y ke yi misali idan likita ne ''dakta sahib'', idan kuma lauya ne su kira shi da ''vakil sahib'', da sauransu.
  • Idan suna son yin magana da shi, sukan ce ''Ji mana'', ko kuma ''kai'', ko su ce ''ji mana'', ko kuma ''ka na ji na''.
  • A wasu yankunan Indiya sukan kira miji da sunan ''dan uwa'', ko ''babban yaya'', ko idan za su yi magana da shi su ce ''ina magana'', da sauransu.

A halin da ake ciki masu daukar hotunan bidiyo na sa kai, suka fara wani gangami a wasu kauyukan Indiya, don ganin ko za su iya rage al'adar .

A watan Oktobar da ya gabata wata ma'aikaciyar sakai mai sunan Rohini Pawar wadda ke zaune a kusa da wani kauye da ke yammacin birnin Pune, ta tayar da maganar rage al'adar sakaya sunan miji, a wani taro da aka shirya na mata zalla don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi matan.

Amma kafin ta gabatar da maganar, sai da ta fara gwadawa da kanta.

Pawar ta shaidawa BBC cewa, an yi mata aure tana da shekara 15, kuma cikin shekara 16 da ta yi a gidan aure ba ta taba fadar sunan mijinta Prakash ba.

Farkon aurensu tana kiransa da sunan ''baba'', saboda 'ya'yan 'yan uwansa haka su ke kiran sa. Wasu lokutan ta kan kira shi da suna 'aaho'', ma'ana 'kai' da yaren Marathi na kasar.

Prakash ya na jin dadin yadda ta ke kiran sunansa, amma kuma sauran mutanen kauyen ba su so hakan ba.

Hakkin mallakar hoto Video Volunteers
Image caption Rohini Pawar: Mutane na yawan tambayar ko me ya sa muke kiran sunan haka?

Matan da suke tattaunawa a kan batun sun yi na'am da wannan sauyi.

"A ranar mun yi dariya, mun yi raha da junanmu. Ko wacce ka kalla tana cike da farin ciki. A karon farko a rayuwarmu mun fadi sunayen mazajenmu duk da a tsakaninmu abin ya faru, amma dai akwai annashuwa kan hakan,'' in ji Pawar, tana kuma kyalkyata dariya.

"Sai kuma muka kunna abin daukar hoton bidiyo, muka umarci ko wacce mace ta fadi sunan mijinta cikin yanayi guda uku: yanayin soyayya, da bakin ciki da kuma farin ciki.''

"Daya daga cikin matan, ta koma gida cike da nishadi, ai tana ganin mijinta sai kawai cikin zumudi ta fadi sunansa, ba kuma tare da bata lokaci ba ya falla mata mari.''

''Ya kuma ce idan ta kuskura ta kara fadar sunansa, sai ya lakada mata duka.''

Hakkin mallakar hoto Video Volunteers

Lamarin ba haka ya ke ba a cikin birane, don ba wani abu ba ne dan mace ta fadi sunan mijinta, wanda hakan ga matan da ba su waye ba ko kuma da ba 'yan boko ba su ke kallo a matsayin babban zunubi.

Da alama a hankali al'adar fadar sunan miji na dan raguwa tsakanin matan karkara, musamman wadanda ke cudanya da wasu mutanen na birane.

Wata ma'aikaciya ta ce mijin da ta aura abokin aikinta ne, kuma ta dade tana kiran sunansa don haka ba ta ga dalilin da zai sa yanzu da suka yi aure za ta daina fadar sunansa ba.

Amma duk da haka farfesa A R Vasavi, ya ce har yanzu wasu mutanen ba lallai sai a kauyuka ba su kan sakaya sunan mazajensu.

Rohani Pawar ta ce duk da cewa miliyoyin mata na ci gaba da al'adar kin fadar sunan miji, kuma a kan samu sauyi a wasu wuraren na fadar haka, ba a zuwa ko ina idan sabuwar amarya ta fadi sunan mijinta uwar mijin da sauran dattijan gida suke taka mata burki, ba kuma za ta sake fadar sunan ba.

"Akwai matukar wahala a kawo sauyi a lokaci daya, mutane na yawan tambayar mata wai menene dalilin da ya sa muka nace kan lallai sai an fadi sunan miji? Ko akwai wata boyayyar manufa kan hakan? ''

A ganina idan ana son kawo sauyi, ana farawa ne daga batutuwa masu sassauci zuwa manya.''

Akwai jan aiki matuka, kafin a cimma nasarar abin da ake son sauyawa.

Join the conversation - find us on Facebook, Instagram, Snapchat and Twitter.

Labarai masu alaka