Me za a yi don kauce wa ambaliyar ruwa a Najeriya?

People walk on a flooded road at Okokomaiko in Ojo district of Lagos, on May 31, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Torrential rainfall left many homes, shops and roads flooded in Lagos

Al'ummar Najeriya na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa da zai iya biyo bayan damuna da za ta zo da ruwa kamar da bakin kwarya.

Tun daga farko watan Yuli ne gwamnatin kasar ta fitar da gargadin cewa 30 daga cikin jihohi 36 na fuskantar wannan barazana.

A yanzu haka ma jihohi 16, ciki har da cibiyar kasuwancin kasar, Legas, sun samu matsalar ambaliyar ruwa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce shekara biyar da suka gabata ne aka samu mafi munin ambaliyar ruwa a Najeriya cikin fiye da shekara 40, kuma ta yi yi sanadin mutuwar mutum 431, sannan kusan mutum miliyan biyu ne suka rasa muhallansu.

Hanyoyin da suka kamata 'yan Najeriya su bi domin kauce wa ambaliyar ruwa duk shekara.

Wanne irin muni ambaliyar ruwa ta yi a wannan shekarar?

Akasari damuna na farawa ne daga watan Yuli zuwa watan Satumba a Najeriya, wanda ke sanya al'umma cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa a fadin kasar, inda take sanadin mutuwar mutane da rasa muhallai.

A wannan shekarar, mutane da dama sun mutu a fadin kasar, yayin da daruruwan gidaje suka rushe.

Image caption Motoci sun kusa nutsewa sanadiyar ambaliyar ruwan

Sa'adu Abubakar, mai shekarar 37 da ke sayar da shayi, ya rasa yaransa shida da matansa biyu, bayan da ambaliyar ruwa ta abka wa gidansa cikin dare a garin Suleja, kusa da babban birnin tarayya Abuja.

Ya shaida wa BBC cewa, "Ina rike da yarana biyu, amma karfin ruwan ya sa suka kubuce daga hannuna."

Malam Abubakar ya kara da cewa, "Na yi ta addu'o'i a wannan lokacin, sannan sai da gari ya waye muka gano gawarwakin iyalan nawa daga wani waje mai dan nisa daga gidana."

Image caption Yadda ruwa ke gudu a titunan birnin Suleja

Wani mazaunin Suleja kuma ya shaida wa BBC cewa, "An soma ruwan ne da misalin karfe 11:30 na dare, inda muka ji wata kara mai karfi. Kawai kafin na san me nake ciki sai na ji tsundum cikin ruwa har wuya."

Ya kara da cewa, "Ba mu iya daukar komai ba cikin kayanmu. Duk da cewa na gina gidana da bulo masu kwari, sai da ruwan ya rusa shi."

"Muna bukatar taimako, har yanzu ba ma samun yin girki ba, sai taimako da muke samu daga wurin mutane," in ji shi

Wannan lamari da ya faru a Suleja na daga cikin mafi munin ambaliyar ruwa a Najeriya, inda duk da rayuka da muhallan da aka rasa, gwamnati har yanzu ba ta dauki wasu kwararan matakai na ganin an kaucewa sake aukuwarsa ba.

Wadanne wurare ne suka fi fuskantar matsalar?

Jihar Naija da ke arewacin kasar ce ke da mafi yawan mutanen da lamarin ya shafa, inda hukumomi suka tabbatar da mutuwar mutum 15 da wasu da dama da suka samu rauni.

Sauran jihohin da lamarin ya shafa yawanci na daga kudancin kasar ne, wadanda ke kusa da tekun Naija, ciki har da jihar Legas.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ruwa kamar da bakin kwarya ya janyo ambaliyar ruwa a gidajen mutane da shaguna da tituna a Legas

Meya sa ambaliyar ruwan ta yi muni?

Yawan aukuwar ambaliyar ruwan ya bambanta daga yanki zuwa yanki, amma damunar ta fi tsanani a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumba, inda mutanen da ke zama a yankunan da ke da barazana ke zama cikin zulumi.

Ruwa kamar da bakin kwarya da toshewar magudanan ruwa ne suka janyo ruwa ya kauce hanya zuwa kasuwanni da gidajen mutane.

Aliyu Salisu Barau, wani kwararre a tsare-tsaren gidajen garuruwa, ya shaida wa BBC cewa hukumomin Najeriya da al'ummar kasar ba su yi wani tanadi na musamman domin fuskantar irin wannan ibtila'i ba.

A cewarsa, "Idan har ana so a tunkari matsalar ambaliyar ruwa, sai an dauki lokaci ana shiri."

Malam Barau ya kara da cewa, "Yawanci hukumomi ba sa gina magudanan ruwa masu inganci, har sai damuna ta gabato."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magudanar ruwa maras inganci na daga cikin abubuwan da ke janyo ambaliyar ruwa

Yadda al'ummar kasar ke karuwa ma na kara ta'azzara matsalar.

A yanzu, al'ummar Najeriya sun kai miliyan 180, kuma a kiyasin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, Najeriya na hanyar zamowa kasa ta uku da ta fi yawan al'umma a duniya, nan da shekara 2050, inda za ta yi wa Amurka fintinkau.

Hakan zai iya sanya matsin lamba sosai kan filaye a kasar, saboda mutane za su bukaci wuraren gina gidajensu.

Amma kuma, tushen matsalar ita ce rashin ingantaccen tsara gidaje, da kuma kasawar hukumomi wajen daukar darasi daga abubuwan da suka faru a baya.

Wasu cikin 'yan kasar kuma na da dabi'ar zubar da shara a kan tituna, wanda hakan ke kara bata hanyoyin wucewar masai, da kuma toshe magudanan ruwa.

Ina labarin madatsun ruwa kuma?

Ana yi wa madatsun ruwa a Najeriya kallon daya daga cikin matsalolin.

Ana amfani da su wajen noman rani da noman kifi, yayin da ake samu wasu da ke kusa da birane da kauyuka.

Amma kuma masu fashin baki sun ce madatsun ruwan ba sa samun kula, wanda ke sa su su fashe lokacin damina, kuma hakan ke sanadiyyar ambaliyar ruwa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu bayan fashewar wata madatsar ruwa sanadiyyar ruwan sama mai karfi a jihar Oyo, a 2011

Madatsar Lagdo da ke kasar Kamaru da ke makwabtaka na cike da barzanar ambaliyar ruwa, ganin yadda ya ke hanyar tekun Benue, wanda ya ratsa har cikin Najeriya.

Hukumomin Kamaru sun gargadi Najeriya da cewa, za su saki ruwan da ya yi wa madatsar ta Lagdo yawa.

Bugu da kari, hukumomin Najeriya ba su yi wani tanadi na musamman ba wajen kwashe mutanen a yankunan da ambaliyar ka iya shafa, duk da cewa an yi gargadin tun da wuri.

Menene gwamnatin Najeriya ya dace ta yi?

Kwararru sun ce ya kamata a yi kwakkwarar tanadi domin kaucewa yawamn al'ummar da aka shafe shekaru ana samu, kazalika, rasa muhallai na iya raguwa idan har mutane sun bi doka da ka'idojin wajen ginagidajen su, ba tare da cin hanci da karkata hanya ba.

Image caption Ambaliyar ruwa da ruwa kamar da bakin kwarya na rusa gidanjen mutane

Za a iya samun raguwa a mutanen da suka rasu da kuma irin illar da garuruwa ko kauyuka ke iya fuskanta idan har gwamnati ta tabbatar ta kafa matakai na kaucewa ibti'la'in.

Fadakar da mutane da kuma basu kwarin gwiwa wajen neman ilimi kan muhallansu.

Idan har ba a dauki kwararan matakai ba, kwararru sun yi gargadin cewa, matsalar ambaliyar ruwa za ta cigaba da sanadin mutuwar mutane da rasa muhallansu.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba