Ko lasisin tukin mota ya kusa daina amfani?

Transportation Secretary Anthony Foxx (R) and Google Chairman Eric Schmidt (L) ride in a Google self-driving car at the Google headquarters on February 2, 2015 in Mountain View, California. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Anan ana gwada wata mota mara matuki ne kirar Google a birnin California

Ta yiwu ba a saba da motoci mara matuki ba a yanzu, amman a shekaru masu zuwa za ku yi ta cin karo da su ko kuma ma amfani da su a kullum. Shin wannan zai kawo karshen amfani da lasisin tuki ne tare da sauya dokokin kan hanya?

An saba ganin wata guntuwar mota tana tafiya kan titin Greenwich, kudu maso gabashin birnin Landan, yayin da take kai abinci ga mazauna unguwar Borough da irin saurin mil hudu cikin ko wacce sa'a.

Bas-bas din biranen Parsi da Helsinki suna jigilar fasinjoji kan ktitunan birnin, yayin da wata doguwar mota mai tayu goma sha takwas take jigilar barasa a kan babbar hanya mai tsawon mil 120 ba tare da matuki ba.

A fadin duniya ana ci gaba da gabatar da ayyuka irin wannan domin samar da fasahar da za ta kawo motoci mara matuki da kuma wasu motocin a kan hanyoyinmu.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wata motar aika da ake gwadawa a Greenwich, Landan

Amman tare da tunanin ko motocin za su yi aiki, akwai wani batun na daban: ta yaya za a kiyaye lafiyar masu tafiya a kasa da masu tukin keke da kuma masu tukin mota?

A yanzu haka cinikin motoci mara matuka ya kai na dubban motoci, amman wani kiyasi na cewa za su iya kai wa miliyan 10 nan da shekarar 2030.

Amman wannan wani dan karamin kashi ne na motoci sama da biliyan daya da a yanzu haka ke kan hanya.

Saboda haka, kalubalen shi ne yadda za a samar wa mutane da kuma motoci mara matuka maslaha a kan hanya da gefen hanya da kuma hanyar keke.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A nan ana gwada wata mota kirar Nissan mara matuki a birnin Landan

Muna da wasu shekaru, kai har gwamman shekaru na warware wannan matsalar da kuma babu alamar samun motoci mara matuka da ka iya aiki ba tare da wani tallafi daga dan adam ba a halin yanzu.

Har yanzu injiniyoyi na aiki domin warware wasu daga cikin matsaloli mafi wuya.

Yi tunanin abin da ka iya faruwa in aka hadu a tsaka-tsaki- a lokacin da direbobi da masu tafiya a kasa suka hadu a lokaci daya, kuma suka yi amafani da gani da alamar hannu da kuma ilhama domin wucewa a hanyar ba tare da samun matsala ba.

Irin wannan tunanin zai kure na'urorin.

Sauran kalubalen sun hada da yanayi da ka iya hana na'u'rar gano abubuwan aiki.

Kuma dole motoci mara matuka su koyi lokacin da za su ki bin dokokin hanya- misali a lokacin da motar ba da agajin gaggawa ke bukatar kowa ya bar kan hanya.

A halin yanzu ana kan gwada motoci mara matuka ne, ana koyon yadda za a yi da irin rashin tabbas da ke da yawa a tuki.

Ba wani abu ba ne da suka riga suka riga suka kware a kai ba, kuma sau da yawa sai mutane sun kawo dauki ga motoci mara matuka domin a kauce wa hatsari.

An samu wasu hadura da suka yi kaurin suna- ciki har da mutuwar da wata motar Teslar ta jawo- yayin da yawancin haduran ke faruwa ne sabo da kura-kuran dan adam- kamar kunna jar fitila.


Motoci mara matuka a fadin duniya

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Daruruwan biliyoyin mil

Jami'ai suna kokarin samun wasu dokokin da za su bayar da damar gwaji a fili, amman wannan ma ka iya kasawa.

Zai dauki daruruwan shekaru na gwaje-gwajen hanya da kuma fiye da daruruwan biliyoyin mil domin tabbatar da cewar motoci mara matuka za su janyo yawan mace-mace.

Maimakon haka, zai iya zama mana dole mu bar motoci mara matuka a wani yanayin, yayin da suke ci gaba da koyo.

A halin yanzu babu wata ka'idar kariya ta kasa-da kasa kan motoci mara matuka - ko wacce kasa take da alhakin rubuta nata dokokin.


Ya batun lasisin tuki kuma?

Wani batun da ba shi da tabbatacciyar amsa shi ne irin da'ar da ya kamata motoci mara matuka su bi.

A sauwake, shin ya kamata ne a sarrafa mota mara matuki ta yadda za ta kauce daga hanya inda za ta sanya rayuwar mutane hudu a hatsari, ko kuma ta ci gaba ta je ta buge iyaye da kuma dan da ke tsallake hanya?

Ganin cewa direbobi suna yanke hukunci ne cikin kasa da dakika daya, ba za mu iya duba ga halayyar mutane ba wajen neman amsa mafi dacewa.

Sauyi daga halin da motoci ke tuka kansu a wani yanayi a tsanake ba tare da tashin hankali ba inda mutane ke zaman ko-ta-kwana zuwa lokacin da motocin za su ta yanke hukunci da kansu, zai kasance wani sauyin da za a yi a hankali.

Masu kera motoci ba za su iya yin watsi da birki da sitiyari ba har sai lokacin da motoci za su iya sarrafa kansu da kansu ba tare da hannun mutum ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka

Karin bayani