Tsawa ta kashe mutane 11 a India

Yadda ruwa ya kusa shanye wani bene a India Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption India ta shafe shekaru da dama bata ga irin wannan yanayi na damuna ba

A kalla mutane 11 ne suka mutu bayan tsawa ta fada kan su, a jihar Odisha da ke Indiya.

Mutanen na aikin noma ne a yayin da ake kwarara ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Jami'ai sun ce wasu mutum 15 kuma sun samu rauni.

An shiga wani yanayi na damina gadan-gadan, inda ake da rahotannin da ke cewa hakan ya jawo matsaloli da dama a wasu jihohin daban-daban, wanda ya kai ga lalacewar tituna da layukan wutar lantarki.

Daminar ta yi sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka shafe shekaru rabon da a ga irinsa.

Rahotanni sun ce kusan mutum 700 ne suka rasu a wannan daminar, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu.

Labarai masu alaka