Nigeria: 'Ba za mu daina neman mai a Borno ba'

Hakkin mallakar hoto NNPC Facebook
Image caption Ma'aikatan jami'ar Maiduguri da na kamfanin NNPC na aiki ne dan gano arbarkatun kasar da ke yankin tafkin Chadi

Shugaban Jami'ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi ya ce suna tare da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) game da neman danyen mai da ake yi a tafkin Chadi bayan wani hari da masu tada kayar baya suka kai kwanakin baya.

Farfesa Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da Karamin Ministan Man Fetur din kasar Dokta Ibe Kachikwu da kuma wasu manyan jami'an NNPC suka kai masa ziyara a karshen makon jiya.

"Al'ummar jami'ar nan sun damu bayan harin da aka kai wa masu aikin neman mai ciki har da wasu ma'aikatan jami'ar. Amma ba za mu janye daga aikin neman man ba. Muna tare da kamfanin NNPC don a koma a ci gaba da aikin neman," in ji farfesan.

Har ila yau, kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa za su taimaka wa iyalan wadanda harin ya shafa da kuma jami'ar.

Hakazalika kamfanin ya ce za su ci gaba aikin neman mai a yankin.

A makon jiya ne kamfanin ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai guda goma da suke masa aiki a jihar Borno.

Rahotanni sun ce sakamakon kwantan baunar da kungiyar ta kai, mutane fiye da 40 ne suka mutu da suka hada da sojoji da kuma 'yan sintiri.

Labarai masu alaka