An kama mutum uku da laifin kisan daliban Jami'ar Fatakwal

An kashe daliban ne saboda zargin sata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kashe daliban ne saboda zargin sata

Wata babbar kotun da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta kama mutum uku da laifin kisan dabilan Jami'ar Fatakwal hudu ta hanyar kona su da wuta.

A shekarar 2012 ne aka kona daliban a kauyen Aluu, lamarin da ya sa aka yi wa batun lakabi da Aluu 4.

An kashe Ugonna Obuzor, Toku Lloyd, Chiadika Biringa, da Tekena Elkanah, bayan an zarge su da laifin yin sata a Aluu, ranar biyar ga watan Oktoban 2012.

Batun dai ya jawo suka sosai a kasar, inda aka rika kiraye-kirayen yi wa daliban adalci.

Alkalin kotun Mai shari'a Nyordee ya kuma wanke hudu daga cikin mutanen da aka zarga da kisan daliban.

A cewar alkalin, masu shigar da kara ba su iya gamsar da kotu kan laifin da ake zargin mutanen hudu da aka wanke ba.

Sai dai ya ce "mutane uku na farko na da laifi dumu-dumu kan kisan daliban."

Masu sharhi a kasar dai na ci gaba da korafi kan yadda ake kwashe shekara da shekaru ba a yanke hukunci kan wasu shari'u ba.

Labarai masu alaka